Hadisai

Babu cuta babu cutarwa, wanda ya cutar Allah Zai mayar masa da sakamakon cutar a kansa, wanda ya tsananta Allah Zai mayar masa da sakamakon tsanantawar a kansa

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce ne a baki dayan ruwayoyin saDar Al-Kutni ne Ya Rawaito shi

Rubutun Larabci

عن أبي سعيد الخدري رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «لَا ضَرَرَ وَلَا ضِرَارَ، مَنْ ضَارَّ ضَرَّهُ اللَّهُ، وَمَنْ شَاقَّ شَقَّ اللَّهُ عَلَيْهِ».

Fassara

Daga Abu sa'id AlKhudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amnicin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Babu cuta babu cutarwa, wanda ya cutar Allah Zai mayar masa da sakamakon cutar a kansa, wanda ya tsananta Allah Zai mayar masa da sakamakon tsanantawar a kansa".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa tunkuɗewa kai da wasu cuta yana wajaba gargwadon nau'o'inta da yadda ta bayyana, baya halatta ga wani ya cutar da kansa ko waninsa daidai wa daida. Kuma ba ya halatta gare shi ya rama cuta da cuta; domin cuta ba a tunkuɗeta da cuta sai dai ta hanyar ƙisasi ba tare da wuce gona da iri ba. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya bayyana narko da faruwar cuta ga wanda yake cutar da mutane, da kuma faruwar wahala ga wanda yake tsanantawa mutane.

Fa'idoji

  • Hani game da ramuwa da sama da abin da aka yi.
  • Allah bai umarci bayainsa da wani abu da zai cutar da su ba.
  • Haramta cuta da cutarwa ta magana ko da aiki ko da bari.
  • Sakamako yana kasancewa daga jinsin aiki, wanda ya cutar Allah Zai haɗa shi da sakamakon cuta, wanda ya tsananta Allah Zai haɗa shi da sakamakon tsanantawa.
  • Daga ƙa'idojin shari'a akwai: "Cuta ana gusar da ita", shari'a ba ta tabbatar da cuta, kuma tana inkarin cutarwa.
Sharhi: العربية

بَيَّنَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنه يَجِبُ دفعُ الضررِ بمختلف أنواعه ومظاهره عن النفس وعن الآخرين، فلا يَحِلُّ لأحدٍ أن يُؤذيَ نفسَه أو غيرَه على حد سواء. ولا يَحلُّ له أن يقابِلَ الضررَ بالضرر؛ لأن الضررَ لا يُزال بالضرر إلا على سبيل القصاص دون تعدٍّ. ثم بيَّنَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم الوعيدَ بحصول الضرر لمن يَضرُّ بالناس، وبحصول المشقة لمن يَشقُّ على الناس.

  • النهي عن المجازاة بأكثر من المِثْل.
  • لم يأمر اللهُ عبادَه بشيء يضرُّهم.
  • تحريم الضرر والضرار بالقول أو بالفعل أو بالترك.
  • الجزاء من جنس العمل، فمن ضارَّ ضارَّه الله، ومن شاقَّ شاقَّه الله.
  • من قواعد الشريعة: أن "الضرر يُزال"، فالشريعة لا تُقِرُّ الضرر، وتنكر الإضرار.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari