Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ مَعْقِلِ بْنِ يَسَارٍ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «الْعِبَادَةُ فِي الْهَرْجِ كَهِجْرَةٍ إِلَيَّ».
Fassara
Daga Ma'ƙil ɗan Yasar - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ibada a cikin rashin zaman lafiya kamar hijira ce zuwa gareni".
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nunar zuwa ibada da yin riƙo da ita a cikin zamanin rashin zaman lafiya da fitina da yaƙe-yaƙe da cakuɗewar al'amuran mutane, kuma cewa ladanta kamar hijira ce zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, hakan domin cewa mutane suna rafkana daga gareta, suna shagaltuwa daga gareta, babu mai ƙoƙari gareta sai ɗaiɗaiku.
Fa'idoji
- Kwaɗaitarwa akan ibada da fuskanta zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki - a kwanukan fitintinu; dan neman kariya daga fitintinu, da kuma kiyayewa daga ɓarna.
- Bayanin falalar ibada a lokutan fitintinu da lokutan rafkana.
- Yana kamata ga musulmi ya kaucewa guraren fitintinu da rafkana.
Sharhi: العربية
أَرْشَدَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم في زمن الهَرْج والفتنة والقتل واختلاط أمور الناس إلى العبادة والتمسك بها، وأنّ أجرها كهجرة إلى النبي صلى الله عليه وسلم، وذلك لأن الناس يغفلون عنها، ويشتغلون عنها، ولا يتفرغ لها إلا أفراد.
- الحث على العبادة والإقبال على الله تعالى أيام الفتن؛ تَحَصُّنًا من الفتن، وحِفْظًا من الفساد.
- بيان فضل العبادة في الفتن وأوقات الغفلة.
- ينبغي للمسلم اعتزال مواطن الفتن والغفلة.