Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما: أَنَّ نَبِيَّ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ يَقُولُ عِنْدَ الْكَرْبِ: «لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ الْعَظِيمُ الْحَلِيمُ، لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ رَبُّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ، لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ رَبُّ السَّمَاوَاتِ وَرَبُّ الْأَرْضِ وَرَبُّ الْعَرْشِ الْكَرِيمِ».
Fassara
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - Cewa Annabin Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cewa a lokacin baƙin ciki: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Mai girma kuma Mai haƙuri, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Ubangijin al'arshi mai girma, babu wani abin bauta da gaskiya sai Allah, Ubangijin sammai, Ubangijin ƙasa, kuma Ubangijin al'arshi mai girma».
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cewa a lokacin tsananin baƙin ciki da takaici gareshi: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah" babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, "Mai girman" daraja, mai girman sha'ani, a cikin zatinSa da siffofinSa da ayyukanSa, "Mai haƙuri" wanda ba Ya gaggauto da uƙuba ga mai saɓo kai Yana jinkirtata, kuma Zai iya yi masa afuwa tare da iko akansa, Shi ne Mai iko - tsarki ya tabbatar maSa akan kowane abu. "Babu abin bautawa da gaskiya sai Ubangijin al'arshi mai girma" Mahaliccin al'arshi Mai girma. "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Ubangijin sammai da ƙasa" kuma Mahaliccin sammai da ƙasa, kuma Mahaliccin kowane abu a cikinsu kuma Mamallakinsa kuma Mai gyara shi , kuma Mai tasarrufi a cikinsa yanda ya so, "Ubangijin al'arshi mai girma" Mahaliccin al'arshi mai girma.
Fa'idoji
- Wajabcin gaggawar komawa zuwa ga Allah da addu'a a lokacin saukar musibu da baƙƙan ciki.
- Anso addu'a da wannan zikirin a lokacin baƙin ciki.
- Al'arshin al-Rahman wanda Ya daidaita akansa - Maɗaukaki - shi ne mafi ɗaukakar ababen halitta kuma mafi girmansu, haƙiƙa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya siffanta shi da cewa shi mai girma ne.
- An keɓanci sammai da ƙasa da ambato; domin cewa sune mafi girman ababen halitta waɗanda ake gani.
- AlƊaibi ya ce: Ya fara da wannan yabon ne da ambato dan ya dace da yaye baƙin ciki; domin cewa shi ne mahukuntar tarbiyya, kuma acikinsa akwai Hailala wacce ta ƙunshi tauhidi wanda shi ne asalin tsarkake-tsarkake masu girma, da girman da yake nuni akan cikar iko, da haƙuri wanda yake nuni akan ilimi, dan jahili ba'a tinanin haƙuri ko kyauta daga gare shi , kuma sune asalin siffofin girmamawa.
Sharhi: العربية
كَانَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم يقول عند اشتداد الكَرْب والغَمِّ عليه: «لا إله إلا الله» لا معبودَ بحق إلا الله، «العظيم» القَدْرِ، الجليل الشأن، في ذاته وصفاته وأفعاله، «الحليم» الذي لا يُعَاجِل العاصي بالعقوبة بل يُؤخّرها، وقد يعفو عنه مع القدرة عليه، فهو القادر سبحانه على كل شيء. «لا إله إلا الله رب العرش العظيم» خالق العرش العظيم، «لا إله إلا الله رب السموات والأرض» وخالق السموات والأرض، وخالق كل شيء فيهما ومالكه ومُصْلِحُه، والمُتصرِّف فيه كيف ما شاء، «رب العرش الكريم» خالق العرش الكريم.
- وجوب الفزع إلى الله بالدُّعَاء عند نزول المصائب والكُرُوْب.
- استحباب الدعاء بهذا الذِّكْر عند الكرب.
- عرش الرحمن الذي استوى عليه جل جلاله هو أعلى المخلوقات وأكبرُها وأعظمُها، وقد وصفه النبي صلى الله عليه وسلم بأنه عظيم وبأنه كريم.
- خص السموات والأرض بالذكر؛ لأنهما من أعظم المخلوقات المشاهدة.
- قال الطيبي: صَدَّرَ هذا الثناءَ بذكر الرب لِيناسب كَشْفِ الكرب؛ لأنه مقتضى التربية، وفيه التهليل المشتمل على التوحيد وهو أصل التنزيهات الجلالية، والعظمة التي تدل على تمام القدرة، والحلم الذي يدل على العلم، إذ الجاهل لا يُتَصَوّر منه حِلْم ولا كرم وهما أصل الأوصاف الإكرامية.