Hadisai

Na haneku da zato; domin cewa zato shi ne mafi karyar zance

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صلى الله عليه وسلم قَالَ: «إِيَّاكُمْ وَالظَّنَّ؛ فَإِنَّ الظَّنَّ أَكْذَبُ الْحَدِيثِ، وَلَا تَحَسَّسُوا، وَلَا تَجَسَّسُوا، وَلَا تَحَاسَدُوا، وَلَا تَدَابَرُوا، وَلَا تَبَاغَضُوا، وَكُونُوا عِبَادَ اللهِ إِخْوَانًا».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Na haneku da zato; domin cewa zato shi ne mafi karyar zance, kada ku yi binciken (aibobin mutane), kada ku yi hassada, kada kujuyawa juna baya, kada ku yi kiyayya, ku zama bayin Allah 'yan uwa".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana hani, yana gargadarwa daga sashin abinda yake kaiwa zuwa rabuwa da gaba a tsakanin musulmai, daga cikin hakan: (Zato) shi ne tuhumane da yake faruwa a cikin zuciya ba tare da wani dalili ba, ya kuma bayyana cewa shi ne mafi karyar zance. Da (Bincike): Shi ne bincike game al'aurorin mutane ta hanyar gani ne ko kasa kunne. Da (bincike): Shi ne bincike daga abinda ya boyu daga al'amura, mafi yawan abinda ake fada a (Tajassus) a sharri ne. Da kuma: Game da (hassada) ita ce kin samuar ni'ima ga wasu. Da kuma: (Juyawa juna baya) shi ne sashi ya bijirewa sashi, ba zai yi sallama ba, ba zai ziyarci dan'uwansa musulmi ba, Da kuma: (kiyayya da juna) kiyayya da gujewa, kamar cutar da wasu ne, da daure fuska da mummunar tarba. Sannan ya fadi wata kalma wacce ta tattaro halayen Musulmai sashinsu tare da sashi da za ta gyara su ita ce:(ku zama bayin Allah 'yan uwa). 'Yan uwantaka tana kulla alakoki dake tsakanin mutane, da suke haduwa da ita, kuma tana kara soyayya da sabawa a tsakaninsu.

Fa'idoji

  • Mummunan zato ba ya cutar da wanda alamominsa suka bayyana daga gare shi, ya wajaba akan muminai su zama masu basira masu fahimta, kada su yaudaru da munanan mutane da kuma fasikai.
  • Abin nufi shi ne gargadarwa daga tuhumar da take zama a cikin zuciya, da kuma nacewa akanta, amma abinda yake bijirowa a cikin zuciya ba ya tabbata to wannan ba'a dorawa da shi.
  • Haramta sabubban kyamar juna da yankewa a tsakanin zamantakewar musulmai, na bincike da hassada da makancinsu.
  • Wasicci da yi wa musulmi mu'amala mu'amalar dan uwa, a nasiha da kauna.
Sharhi: العربية

يَنْهَى النبيُّ صلى الله عليه وسلم ويُحَذِّرُ مِن بعضِ ما يؤدِّي إلى الفُرْقة والعداوة بين المسلمين، ومن ذلك: (الظن) وهو تُهمةٌ تقَعُ في القَلبِ بلا دَليلٍ، وبَيَّنَ أنه مِن أَكْذَب الحديث. وعن (التَّحَسُّس): وهو البحث عن عورات الناس بالعين أو الأذن. و(التَّجَسُّس): وهو البحث عن ما خفي من الأمور، وأكثر ما يقال ذلك في الشر. وعن: (الحسد) وهو كراهية حصول النعمة للآخرين. وعن: (التدابر) بأنْ يَعْرِضَ بعضُهم عن بعض، فلا يسلِّم ولا يزور أخاه المسلم، وعن: (التباغض) والكراهية والنفرة، كأذية الآخرين، والعبوس وسوء المقابلة. ثم قال كلمة جامعة تصلح بها أحوال المسلمين بعضهم مع بعض: (وكونوا عباد الله إخوانًا) فالأخوة رابطة تلتئم بها العلاقات بين الناس، وتزيد المحبة والأُلْفة بينهم.

  • لا يَضُرُّ الظنُّ السيءُ بمَن ظهرتْ منه علاماتُه، وعلى المؤمن أن يكون كَيِّسًا فَطِنًا لا يَنْخدع بأهل السوء والفسوق.
  • المراد التحذير من التهمة التي تستقر في النفس، ومن الإصرار عليها، أما ما يَعرِض في النفس ولا يستقر فهذا لا يُكلف به.
  • تحريم أسباب التنافر والقطيعة بين أفراد المجتمع المسلم، من التجسس والحسد ونحوِهما.
  • الوصية بمعاملة المسلم معاملة الأخ في النصيحة والتَّوَادّ.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari