Hadisai

Wanda ya shiryar a kan wani alheri, to, shi ma yana da kwatankwacin ladan wanda ya aikatashi

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عن أبي مسعود الأنصاري رضي الله عنه قال: جَاءَ رَجُلٌ إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ: إِنِّي أُبْدِعَ بِي فَاحْمِلْنِي، فَقَالَ: «مَا عِنْدِي»، فَقَالَ رَجُلٌ: يَا رَسُولَ اللهِ، أَنَا أَدُلُّهُ عَلَى مَنْ يَحْمِلُهُ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ دَلَّ عَلَى خَيْرٍ فَلَهُ مِثْلُ أَجْرِ فَاعِلِهِ».

Fassara

Daga Abu Mas'ud Al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - sai ya ce: Tafiya ta yanke min, ka ba ni dabbar da za ta ɗaukeni, sai ya ce: "Ba ni da ita", sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah, ni zan shiryar da shi ga wanda zai ba shi dabbar da za ta ɗaukeshi, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Wanda ya shiryar a kan wani alheri, to, shi ma yana da kwatankwacin ladan wanda ya aikatashi".

Sharhi

Wani mutum ya zo ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Lallai cewa dabbata ta halaka, ka ɗorani a kan wata dabbar, kuma ka ba ni wani abin hawan da zai kai ni, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ba shi uzuri cewa ba shi da wani abin da zai dorashi a kansa, sai wani mutum da ya ke wurin ya ce: Ya Manzon Allah, ni zan shiryar da shi ga wanda zai ba shi dabbar da za ta ɗaukeshi, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa ya zama abokin tarayyar mai sadakar a lada; domin ya shiryar da mabuƙacin zuwa gareshi.

Fa'idoji

  • Kwaɗaitarwa a kan shiryarwa ga aikin alheri.
  • Kwaɗaitarwa ga aikata alheri yana daga sabubban taimakekeniya ga zamantakewa da kuma cikarsa.
  • Yalwar falalar Allah - Maɗaukakin sarki -.
  • Hadisin ƙa'ida ne mai gamewa, yana shiga kowa ne ayyukan alheri.
  • Idan mutum bai sami damar tabbatar da buƙatar mai tambaya ba, to, ya shiryar da shi ga waninsa.
Sharhi: العربية

جاء رجلٌ إلى النبي صلى الله عليه وسلم فقال: إني هَلَكَتْ راحلتي، فاحملني على دابةٍ، وأعطني مركوبًا يوصلني، فاعتذر له النبي صلى الله عليه وسلم أنه ليس عنده شيء يحمله عليه، فقال رجلٌ وكان حاضرًا: يا رسول الله، أنا أَدُلُّه على مَن يَحمله، فأخبرَ رسولُ الله صلى الله عليه وسلم أنه شريكٌ للمتصدِّق في الأجر، لأنه دلَّ المحتاجَ عليه.

  • الحث على الدلالة على الخير.
  • الحضُّ على فعل الخير من أسباب تَكَافُل المجتمع المسلم وتكامله.
  • سَعَة فضل الله تعالى.
  • الحديث قاعدة عامة فيدخل فيه كلُّ أعمال الخير.
  • الإنسان إذا لم يتمكَّن مِن تحقيق رغبة السائل، فإنه يَدُلُّه على غيره.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari