Hadisai

Mai yanke zumunci ba zai shiga aljanna ba

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عن جُبَير بن مُطْعِم رضي الله عنه أنه سمع النبي صلى الله عليه وسلم يقول: «لَا يَدْخُلُ الْجَنَّةَ قَاطِعُ رَحِمٍ».

Fassara

Daga Jubair ɗan Mut'im - Allah Ya yarda da shi - cewa ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa; "Mai yanke zumunci ba zai shiga aljanna ba"

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa wanda ya yanke abin da yake wajaba daga 'yan uwansa na haƙƙoƙi, ko ya cutar da su ya munana musu, to, ya cancanci ba zai shiga aljanna ba.

Fa'idoji

  • Yanke zumunci laifi ne daga manyan laifuka.
  • Sa da zumunci yana kasancewa ne gwargwadon abin da aka yi sabo a kansa, yana banbanta da banbantar wurare da zamaninnika da mutane.
  • Sa da zumunci yana kasancewa ne da ziyara da sadaka, da kyautatawa garesu, da duba marasa lafiya, da umartarsu da aikin alheri, da hanasu daga abin ƙi, da makamancin hakan.
  • A duk lokacin da yanke zumuci ya zama da mafi kusanci, to, zai zama ya fi tsananin laifi.
Sharhi: العربية

يُخبِرُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ مَن قَطَع عن أقاربه ما يَجِب لهم من الحقوق، أو آذاهم وأساء إليهم، فهو مُستحق ألَّا يدخلَ الجنة.

  • قطيعة الرحم كبيرة من كبائر الذنوب.
  • صلة الرحم تكون حسب المتعارف عليه، فتختلف باختلاف الأمكنة والأزمنة والأشخاص.
  • صلة الرحم تكون بالزيارة، والصدقة، والإحسان إليهم، وعيادة المرضى، وأمرهم بالمعروف، ونهيهم عن المنكر، وغير ذلك.
  • كلما كانت قطيعة الرحم في الأقرب كانت أشدَّ إثمًا.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari