Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Rubutun Larabci
عن حذيفة رضي الله عنه قال: سمعت النبي صلى الله عليه وسلم يقول: «لَا يَدْخُلُ الْجَنَّةَ قَتَّاتٌ».
Fassara
Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa; "Annamimi ba zai shiga aljanna ba".
Sharhi
(Annabi) Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yana ba da labarin cewa annamimi wanda yake cirato zance a tsakanin mutane da nufin ɓata tsakaninsu shi mai cancanta ne ga uƙubar cewa ba zai shiga aljanna ba.
Fa'idoji
- Annamimanci yana daga manyan zunubai.
- Hani daga annamimanci; saboda abin da ke cikinsa na ɓatawa da cutarwa a tsakaknin ɗaiɗaiku da jama'u.
Sharhi: العربية
يُخبِرُ صلى الله عليه وسلم أنَّ النَّمَّامَ الذي ينقل الكلام بين الناس بقصد الإفساد بينهم بأنه مُستحِقٌّ للعقاب بألَّا يدخلَ الجنة.
- النميمة من كبائر الذنوب.
- النهي عن النميمة؛ لما فيها من الإفساد والضرر بين الأفراد والجماعات.