Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنِ الحُسَينِ بنِ عَلِيٍّ بنِ أَبِي طَالِبٍ رضي الله عنهما قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «الْبَخِيلُ مَنْ ذُكِرْتُ عِنْدَهُ فَلَمْ يُصَلِّ عَلَيَّ».
Fassara
Daga Husaini ɗan Ali ɗan Abu Ɗalib - Allah Ya yarda da su (Husain da Ali) - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Marowaci shi ne wanda aka ambace ni a wurinsa bai yi mini salati ba".
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsoratar akan barin salati gare shi a halin jin sunansa ko alkunyarsa ko siffarsa, ya ce: Marowaci mai cikakkiyar rowa (shi ne) wanda aka ambaceni a wurinsa bai yi mini salati ba; hakan saboda wasu al'amura: Na farko: Cewa hakan rowa ce, da wani abun da ba ya asara saboda shi kaɗan ne ko mai yawa, kuma ba ya bada wata dukiya, kuma ba ya yin wani ƙoƙari. Na biyu: Cewa shi ya yi wa kansa rowa kuma ya haramta mata ladan salati ga Manzonsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; domin cewa shi haƙiƙa ya yi rowa saboda hanuwarsa daga salati gare shi, kuma ya hanu daga bada haƙƙin da bada shi ya wajaba akansa dan ruko da umarni kuma ake samun lada da shi. Na uku: Cewa salati gare shi a cikinsa akwai bada haƙƙin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, shi ne wanda ya sanar damu, kuma shi ne wanda ya shiryar damu, shi ne wanda ya kiramu zuwa ga Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - kuma ya zo mana da wannan wahayin, da kuma wannan shari'ar, shi ne sababin shiriyarmu - bayan Allah - alhrerinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - wanda bai yi masa salati ba zai zama haƙiƙa ya yi wa kansa rowa, kuma ya yi rowa ga AnnabinSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da wani haƙƙin da yana daga mafi ƙasan haƙƙoƙinsa.
Fa'idoji
- Barin salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - take ne na rowa.
- Salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana daga mafificin ayyukan kusanci da kuma ɗa'a a dukkanin lokuta, kuma yana ƙarfafuwa a halin ambatansa.
- Al-Nawawi ya ce: Idan zai yi salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - to ya haɗa tsakanin salati da sallama, kada ya taƙaita akan ɗayansu; kada ya ce: (Allah Ya yi salati gare shi) kadai, ko: (Amnici ya tabbata agare shi) kadai.
- Abul Aliya ya faɗa a cikin faɗinSa: {Lallai Allah da mala'ikunSa suna salati ga wannan Annabi} ya ce: Salatin Allah - Mai girma da ɗaukaka - ga AnnabinSa: YabonSa gare shi, salati daga mala'iku da mutane: Addu'a.
- AlHulaimi ya ce: Ma'anar: "Ya Allah Ka yi salati ga (Annabi) Muhammad": Ya Allah ka girmama shi a duniya da ɗaukaka ambatansa, da bayyanar da Addininsa, da wanzar da shari'arsa, a lahira kuma: Da neman cetansa a sha'anin al'ummarsa, da gwaggwaɓa ladansa da sakamakonsa, da bayyanar da falalarsa ga na farko da na karshe da matsayi abin yabo, da gabatar da shi akan dukkan makusanta masu halartowa.
Sharhi: العربية
حَذَّرَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم مِن تَرْك الصلاة عليه حال سَمَاع اسمه أو كُنْيَتِه أو وصفه، وقال: البَخيل كامل البُخْل مَن ذُكرتُ عنده فلم يُصلِّ عليّ؛ وذلك لأمور: الأول: أنه بُخْلٌ بشيءٍ لا يَخْسَر بسببه قليلًا ولا كثيرًا، ولا يَبذُل مالًا، ولا يَبذُل جُهْدًا. الثاني: أنه بَخِلَ على نفسه وحَرَمَها أجرَ الصلاة على رسوله صلى الله عليه وسلم؛ لأنه بامتناعه من الصلاة عليه قد شَحَّ وامتنع من أداء حقٍّ يَتَعَيَّنُ عليه أداؤه امتثالًا للأمر وينال به الأجر. الثالث: أنَّ الصلاة عليه فيها أداء بعض حقِّ النبي صلى الله عليه وسلم، فهو الذي عَلَّمنا، وهو الذي أرشدَنا، وهو الذي دعانا إلى الله تبارك وتعالى، وجاءنا بهذا الوحي، وهذه الشَّريعة، فهو سبب هدايتنا -بعد الله تبارك وتعالى- ومَن لم يُصلِّ عليه يكون قد بَخِل على نفسه، وبَخِل على نبيِّه صلى الله عليه وسلم بحقٍّ هو من أدنى حقوقه.
- تَرْك الصلاة على النبي صلى الله عليه وسلم عنوان الشُّحِّ.
- الصلاة على النبي صلى الله عليه وسلم من أفضل القُرُبات والطاعات في جميع الأوقات، ويتأكّد حالَ ذِكْرِه.
- قال النووي: إذا صلى على النبي صلى الله عليه وسلم فليَجمع بين الصلاة والتسليم، ولا يَقتصر على أحدِهما؛ فلا يَقل: (صلى الله عليه) فقط، ولا: (عليه السلام) فقط.
- قال أبو العالية في قوله: (إن الله وملائكته يصلون على النبي) قال: صلاة الله عز وجل على نبيه: ثناؤه عليه، والصلاة من الملائكة والبشر: الدعاء.
- قال الحليمي: فمعنى «اللهم صلّ على محمد»: اللهم عظّمه في الدنيا بإعلاء ذِكْرِه، وإظهار دينه، وإبقاء شريعته، وفي الآخِرة: بِتَشْفِيْعِهِ في أُمَّتِهِ، وإِجْزَال أجره ومثوبته، وإبداء فضله للأولين والآخرين بالمقام المحمود، وتقديمه على كافة المقربين الشهود.