Hadisai

Wanda ya yanki haƙƙin wani mutum musulmi da rantsuwarsa, to haƙiƙa Allah Ya wajabta wuta gare shi, kuma Ya haramta masa aljanna" sai wani mutum ya ce: Koda wani abune ɗan kaɗan ya Manzon Allah? ya ce: "Koda kara ne na itaciyar ƙirya

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عن أَبِي أُمَامَةَ إِياسِ بنِ ثَعْلَبَةَ الحَارِثِيِّ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَنِ اقْتَطَعَ حَقَّ امْرِئٍ مُسْلِمٍ بِيَمِينِهِ، فَقَدْ أَوْجَبَ اللهُ لَهُ النَّارَ، وَحَرَّمَ عَلَيْهِ الْجَنَّةَ» فَقَالَ لَهُ رَجُلٌ: وَإِنْ كَانَ شَيْئًا يَسِيرًا يَا رَسُولَ اللهِ؟ قَالَ: «وَإِنْ قَضِيبًا مِنْ أَرَاكٍ».

Fassara

Daga Abu Umama Iyas ɗan Sa'alaba alHarisi - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya yanki haƙƙin wani mutum musulmi da rantsuwarsa, to haƙiƙa Allah Ya wajabta wuta gare shi, kuma Ya haramta masa aljanna" sai wani mutum ya ce: Koda wani abune ɗan kaɗan ya Manzon Allah? ya ce: "Koda kara ne na itaciyar ƙirya".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargaɗar daga yin rantsuwa da Allah akan ƙarya kuma yana sane, hakan dan yankar haƙƙin wani mutum musulmi, domin cewa sakamkon hakan shi ne cancantar wuta, da haramta aljanna, kuma shi yana daga manyan zunubai. Sai wani mutum ya ce ya Manzon Allah: Koda abinda aka rantse akan shi ɗin wani abune dan kaɗan? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Koda hakan ya zama a itacen asuwakin da ake cira ne daga bishiyar ƙirya.

Fa'idoji

  • Gargaɗarwa daga cin haƙƙoƙin wasu, da kwaɗayi akan maida su ga masu su duk ƙarancinsu kuwa, kuma hukuncin alƙali da kuskure ba ya halattawa mutum abinda bai kasance nasa ba ne.
  • Nawawi ya ce: Kaurara haramcin haƙƙoƙin musulmai, kuma cewa shi babu banbanci tsakanin haƙƙi kaɗan da mai yawa; saboda faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: "Koda ya kasance kara ne na itaciyar ƙirya".
  • Nawawi ya ce: Wannan uƙubar ga wanda ya yanki haƙƙin musulmi ne kuma ya mutu kafin tuba, amma wanda ya tuba ya yi nadama akan aikinsa kuma ya maida haƙƙin zuwa ga maishi ya warware daga gareshi kuma ya yi niyya akan cewa ba zai koma ba to haƙiƙa zunubin ya saraya daga gare shi.
  • Alƙali ya ce: Keɓance musulmi dan kasancewarsu sune waɗanda ake yi wa magana kuma waɗanda ake mu'amala da su a shari'a a game, badan cewa wanin musulmi saɓaninsa ba ne, kai hukuncinsa (irin) hukuncinsane a cikin hakan.
  • Nawawi ya ce: Karya shi ne bada labari daga abu akan saɓanin haƙiƙaninsa, da gangan ne ya kasance ko akan rafkanuwa, daidai ne bada labarin ya kasance daga abinda ya wuce ne ko abinda za'a fuskanta nan gaba.
Sharhi: العربية

حَذَّرَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم مِن الحَلِف بالله كاذبًا عالمًا وذلك لاقتطاع حقِّ امرئ مسلم، فإنّ جزاء ذلك استحقاق النار، والحِرْمان من الجنة، وهو من كبائر الذنوب. فقال رجل يا رسول الله: وإن كان المَحْلُوف عليه شيئًا قليلًا؟ فقال صلى الله عليه وسلم: حتى لو كان ذلك في عُوْد السِّوَاك الذي يُؤخذ من شجرة الأراك.

  • الحذر من أخذ حقوق الآخرين، والحرص على أدائها لأصحابها مهما قَلَّتْ، وأنَّ حكم الحاكم بالخطأ لا يُبيح للإنسان ما لم يكن له.
  • قال النووي: غلظ تحريم حقوق المسلمين، وأنه لا فرق بين قليل الحق وكثيره؛ لقوله صلى الله عليه وسلم: "وإن قضيبًا من أراك".
  • قال النووي: هذه العقوبة لمن اقتطع حق المسلم ومات قبل التوبة، أما من تاب فندم على فعله وردَّ الحق إلى صاحبه وتَحَلَّل منه وعزم على أن لا يعود فقد سقط عنه الإثم.
  • قال القاضي: تخصيص المسلم لكونهم المخاطبين وعامة المتعاملين في الشريعة، لا أنَّ غير المسلم بخلافه، بل حُكمُه حُكمُه في ذلك.
  • قال النووي: الكذب هو الإخبار عن الشيء على خلاف ما هو، عمدًا كان أو سهوًا، سواء كان الإخبار عن ماض أو مستقبل.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari