Hadisai

Lallai mafi ƙiyayyar mutane a wurin Allah (shi ne) mai taurin kai mai tsananin husuma

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عن عائشة رضي الله عنها عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «إِنَّ أَبْغَضَ الرِّجَالِ إِلَى اللهِ الْأَلَدُّ الْخَصِمُ».

Fassara

Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a greshi - ya ce: "Lallai mafi ƙiyayyar mutane a wurin Allah (shi ne) mai taurin kai mai tsananin husuma".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa Allah - Mai girma da ɗaukaka - yana ƙin mai tsananin husuma, kuma mai yawaitata daga cikin mutane, wanda ba ya karɓar jawuwa ga gaskiya, kuma yana ƙoƙarin tunkuɗeta da jayayyarsa, ko ya yi husuma da gaskiya, sai dai cewa yana kai matuƙa a cikin husuma, kuma yana fita daga iyakar daidaituwa, yana jayayya ba tare da ilimi ba.

Fa'idoji

  • Neman haƙƙin wanda aka zalunta da gaskiya ta hanyar kai ƙara, ba ya shiga cikin babin husumomi ababen zargi.
  • Jayayya da husuma suna daga illolin harshe waɗanda suke sabbaba rabuwa da juya baya a tsakaknin musulmai.
  • Jayayya abar yabo ce, idan ta kasance a kan gaskiya ne kuma usulubinta mai kyau, kuma tana kasancewa abar zargi idan ta kasance don dawo da gaskiya ne da tabbatar da ɓarna, ko ta kasance ba tare da hujja ba ko dalili.
Sharhi: العربية

يُخْبِرُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ الله تبارك وتعالى يُبغِض مِن الناس شديدَ الخُصُومةِ وكثيرِها، الذي لا يَقبلُ الانقيادَ للحق، ويُحاولُ دفعَه بجَدَلِه، أو يخاصم بحق لكنَّه يُبالِغُ في الخصومة ويخرج عن حدِّ الاعتدال، ويجادل بغير علم.

  • لا يدخلُ في بابِ الخصومات المذمومةِ مطالبةُ المظلوم بحقٍّ له بطريق المرافعات الشرعية.
  • الجدل والخصومة من آفات اللسان التي تُسبب الفرقة والتدابر بين المسلمين.
  • المجادلة محمودة إذا كانت في الحق وأسلوبها حسن، وتكون مذمومة إذا كانت لرد الحق وتثبيت الباطل، أو كانت بغير حجة ولا برهان.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari