Hadisai

Kunya tana daga imani

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عن عبد الله بن عمر رضي الله عنهما قال: سَمِعَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رَجُلًا يَعِظُ أَخَاهُ فِي الْحَيَاءِ، فَقَالَ: «الْحَيَاءُ مِنَ الْإِيمَانِ».

Fassara

Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ji wani mutum yana yi wa ɗan uwansa wa'azi game da kunya, sai ya ce: "Kunya tana daga imani".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ji wani mutum yana yi wa wani ɗan uwansa nasihar cewa ya bar yawan kunya! sai ya bayyana masa cewa kunya tana daga imani, kuma ba ta zuwa sai da alheri. Kunya ɗabi'a ce da take sa aikata mai kyau da barin mummuna.

Fa'idoji

  • Abin da zai hana ka alheri ba a ambatonsa kunya, kai ana ambatonsa tsoro da gajiyawa da rauni da ragonta.
  • Kunyar Allah - Mai girma da daukaka - tana kasancewa ne da aikata abubuwan da aka umarta, da barin abubuwan da aka hana.
  • Kunyar ababen halitta tana kasancewa ne da girmamasu, da saukar da su masaukansu, da nisantar abin da zai munana a al'adance.
Sharhi: العربية

سَمِعَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم رجلًا ينصح أخاه أن يترك كثرةَ الحياء! فبَيَّن له أن الحياء من الإيمان، وأنه لا يأتي إلا بخير. والحياء خُلقٌ يَحْمِلُ على فِعْل الجميل وترك القبيح.

  • ما يَمنعُك من الخير لا يُسمَّى حياءً، بل يُسمى خَجَلًا وعَجْزًا وخَوَرًا وجُبْنًا.
  • الحياء من الله عز وجل يكون بفعل المأمورات، وترك المحظورات.
  • الحياء مِن الخَلق يكون باحترامهم، وإنزالهم منازلهم، واجتناب ما يقبح عادةً.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari