Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عن أبي الدرداء رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «مَنْ رَدَّ عَنْ عِرْضِ أَخِيهِ رَدَّ اللهُ عَنْ وَجْهِهِ النَّارَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ».
Fassara
Daga Abu Al-darda - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gatreshi - ya ce: "Wanda ya kare mutuncin ɗan uwansa Allah Zai kare fuskarsa daga wuta a ranar al-ƙiyama".
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa wanda ya kare mutuncin ɗan uwansa musulmi a bayan idonsa ta hanyar hana zarginsa ko munana masa, to, lallai Allah Zai kareshi daga azaba a ranar al-ƙiyama.
Fa'idoji
- Hani daga magana a kan mutuncin musulmai.
- Sakamako yana kasancewa ne daga jinsin aiki, wanda ya kare mutuncin ɗan uwansa Allah Zai kareshi daga wuta.
- Musulunci addinin 'yan uwantaka ne da taimakekeniya a tsakanin ma'abotansa.
Sharhi: العربية
يُخْبِرُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ مَن دافَعَ عن عِرْضِ أخيه المسلم في غَيْبته بمنع ذَمِّهِ أو الإساءة إليه، فإنَّ اللهَ يَرُدُّ عنه العذابَ يومَ القيامة.
- النهي عن الكلام في أعراض المسلمين.
- الجزاء من جنس العمل، فمن رَدَّ عن عِرض أخيه ردَّ الله عنه النار.
- الإسلام دين التآخي والتناصُر بين أهله.