Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «أَكْمَلُ الْمُؤْمِنِينَ إِيمَانًا أَحْسَنُهُمْ خُلُقًا، وَخَيْرُكُمْ خَيْرُكُمْ لِنِسَائِهِمْ».
Fassara
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Mafi cikar muminai a imani shi ne mafificinsu a kyawawan ɗabi’u, mafificinku shi ne mafificinku ga iyalinsa.
Sharhi
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayanin mafi cikar imani a cikin mutane shi ne wanda ɗabi’unsa suka kyautata, ta hanyar sakin fuska, da bayar da abu mai kyau, da kyakkyawar magana, da barin cutarwa. Mafi alherin muminai shi ne mafi alherinsu ga iyalansa, kamar matarsa da ‘ya'yansa mata, da ‘yan’uwansa mata, da danginsa mata, domin su ne suka fi kowa haƙƙin a kyautata musu.
Fa'idoji
- Falalar kyawawan dabi’u da cewar suna cikin imani.
- Aiki yana cikin imani, shi kuma imani yana ƙaruwa yana raguwa.
- Musulunci ya darajta mace, ya kwaɗaitar a kan kyautata musu.
Sharhi: العربية
يُخْبِرُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ أَكْمَلَ الناس إيمانًا مَن حَسُنَ خُلُقُه، وذلك بطَلَاقَةِ الوجه، وبذل المعروف، وحسن الكلام، وكف الأذى. وخَيْرَ المؤمنين خيرُهم لنسائِهِ، كزَوجتِه وبَناتِه وأخواتِه وقَريباتِه؛ لأنهن مِن أحقِّ الناس بحُسْنِ الخُلُق.
- فضيلة الأخلاق الحسنة وأنها من الإيمان.
- العمل من الإيمان، والإيمان يزيد وينقص.
- إكرام الإسلام للمرأة والترغيب في الإحسان إليها.