Hadisai

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya la'anci mai yin ƙarin gashi da wacce ta nemi a yi mata ƙarin gashi, da mai yin zane a jiki da wacce ta nemi a yi mata

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عن عبد الله بن عمر رضي الله عنهما قال: لعن النبي صلى الله عليه وسلم الوَاصِلَةَ والمُسْتَوْصِلَةَ، والوَاشِمَةَ والمُسْتَوشِمَةَ.

Fassara

Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya la'anci mai yin ƙarin gashi da wacce ta nemi a yi mata ƙarin gashi, da mai yin zane a jiki da wacce ta nemi a yi mata.

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi addu'ar tsinuwa da korewa da nisantarwa daga rahamar Allah - Maɗaukakin sarki - akan nau’uka huɗu: Na farko: Mai yin ƙarin gashin kanta ko ga waninta da wani gashin daban. Na biyu: Mai neman a yi mata ƙarin gashi da buƙatar waninta cewa ya yi mata ƙarin gashi da wani gashin daban. Na uku: Al-Washimah ita ce wacce take aikin kafa allura a wani wuri na jiki, kamar fuska ko tafi ko ƙirji, sai ta sa kwalli ko makamancinsa a cikinsa, har sai gurbinsa ya yi shuɗi, ko ya yi kore; dan neman ado da kuma kyau. Na huɗu: Al-Mustaushimah ita ce wacce take son a yi mata zanen. Waɗannan ayyukan suna daga cikin manyan zunubai.

Fa'idoji

  • Ibnu Hajar ya ce: Abinda aka hana a cikin hakan shi ne ƙarin gashi da gashi, idan ta ƙara gashin kanta bada gashi ba (kamar) da gyalle ko waninsa to ba ya shiga cikin hanin.
  • Haramcin taimakekeniya akan saɓo.
  • Hani daga canja halittar Allah; domin cewa shi ƙarya ne da kuma algus.
  • Halaccin tsinewa wanda Allah da manzonSa suka tsinewa ta hanyar gamewa.
  • Ɗaura Baruka (wigi) a wannan zamanin yana shiga cikin ƙarin gashin da aka haramta, ita abar haramtawa ce dan abinda ke cikinta na kamanceceniya da kafirai da algus da kuma maguɗi.
  • AlKhaɗɗabi ya ce: kaɗai narko mai tsanani ya zo a cikin waɗannan abubuwan; dan abinda ke cikinsu na algus da yaudara, da a ce an yi rangwame a cikin wani abu daga garesu da ya zama tsani zuwa neman halatta waninsu na nau'ikan algus, haka kuma dan abinda ke cikinsu na canja halitta, akwai nuni zuwa ga haka a cikin hadisin Ibnu Mas'ud da faɗinsa: "Masu canja halittar Allah", Allah ne mafi sani.
  • AlNawawi ya ce: Hakan haramun ne akan wacce ta yi da wacce aka yi wa, kuma gurin da aka zana ɗin yana zama najasa, idan zai yi wu a gusar da shi da magani to wajibi ne, idan ba zai yi wu ba sai da ciwo, idan ya ji tsoron ɓaci ko rasa gaɓa ko amfanin (gaɓar) ko wani abu mai muni a cikin gaɓar a zahiri to gusar da shi ba ya wajaba, idan ya tuba wani laifi ba zai ragu daga gare shi ba, idan ba ya jin tsoron wani abu daga hakan to gusar da shi ya wajaba kuma zai yi saɓo idan ya jinkirta gusarwar.
Sharhi: العربية

دعا النبي صلى الله عليه وسلم باللعن والطرد والإبعاد من رحمة الله تعالى على أربعة أصناف: الأول: الواصلة لِشَعَرِ نفسها أو غيرِها بشعر آخر. الثاني: والمستوصلة بطلب غيرها أن يصل بشعرها شعرًا آخر. الثالث: الواشمة التي تقوم بِغَرْزِ الإبرة في موضع من البدن، كالوجه أو الكف أو الصدر، ووضع كُحْلٍ أو نحوه فيه، حتى يَزْرَقَّ أَثَرُه، أو يَخضرّ؛ طلبًا للزينة والجمال. الرابع: المستوشمة التي تطلب أن يُفعل بها الوشم. وهذه الأعمال من كبائر الذنوب.

  • قال ابن حجر: أن الممتنع من ذلك وَصْلُ الشعر بالشعر، وأما إذا وصلت شعرها بغير الشعر من خِرْقة وغيرها فلا يدخل في النهي.
  • تحريم التعاون على الإثم.
  • النهي عن تغيير خلق الله؛ لأنه تزوير وتدليس.
  • جواز لعن من لعنه الله ورسوله على سبيل العموم.
  • يدخل في الوصل المحرم في زمننا هذا لُبْسُ البَارُوْكة، وهي محرمة لما فيها من التشبه بالكفار والغش والتدليس.
  • قال الخطابي: إنما ورد الوعيد الشديد في هذه الأشياء؛ لما فيها من الغش والخداع، ولو رخص في شيء منها لكان وسيلة إلى استجازة غيرها من أنواع الغش، ولما فيها من تغيير الخلقة، وإلى ذلك الإشارة في حديث ابن مسعود بقوله: "المُغيِّرات خلق الله"، والله أعلم.
  • قال النووي: وهو حرام على الفاعلة والمفعول بها، والموضع الذي وشم يصير نجسًا، فإن أمكن إزالته بالعلاج وجبت وإن لم يمكن إلا بالجرح، فإن خاف منه التلف أو فوت عضو أو منفعته أو شيئًا فاحشًا في عضو ظاهر لم يجب إزالته، وإذا تاب لم يبق عليه إثم وإن لم يخف شيئًا من ذلك لزمه إزالته ويعصي بتأخيره. انتهى.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari