Hadisai

Duk wanda ya fita daga biyayya, ya kuma rabu da jama'a sai ya mutu, to, ya mutu irin mutuwar Jahiliyya

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عن أبي هريرة رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم أنه قال: «مَنْ ‌خَرَجَ ‌مِنَ ‌الطَّاعَةِ، وَفَارَقَ الْجَمَاعَةَ فَمَاتَ، مَاتَ مِيتَةً جَاهِلِيَّةً، وَمَنْ قَاتَلَ تَحْتَ رَايَةٍ عِمِّيَّةٍ، يَغْضَبُ لِعَصَبَةٍ، أَوْ يَدْعُو إِلَى عَصَبَةٍ، أَوْ يَنْصُرُ عَصَبَةً، فَقُتِلَ، فَقِتْلَةٌ جَاهِلِيَّةٌ، وَمَنْ خَرَجَ عَلَى أُمَّتِي، يَضْرِبُ بَرَّهَا وَفَاجِرَهَا، وَلَا يَتَحَاشَى مِنْ مُؤْمِنِهَا، وَلَا يَفِي لِذِي عَهْدٍ عَهْدَهُ، فَلَيْسَ مِنِّي وَلَسْتُ مِنْهُ».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Duk wanda ya fita daga biyayya, ya kuma rabu da jama'a sai ya mutu, to, ya mutu irin mutuwar Jahiliyya, wanda ya yi yaƙi ƙarƙashin makauniyar tuta, yana fushi saboda ƙabilanci, ko yake kira zuwa ƙabilanci, ko yake taimakon ƙabilanci, sai aka kashe shi, to, kisa ne na Jahiliyya, wanda ya yi fito na fito da al'ummata yake dukan mutumin kirkinta da fajirinta, ba ya kiyaye wa tsakanin mumininta, kuma ba ya cika alkawari ga ma'abocin alkawari (kafirin amana), to, wannan ba ya tare da ni, ni ma ba na tare da shi".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa wanda ya fita daga biyayyar majiɓinta al'amura, kuma ya rabu da jama'ar musulunci wacce ta haɗu a kan caffar (mubaya’a) shugaba, sai ya mutu a kan wannan halin na rabuwa da rashin biyayya, to, ya mutu irin mutuwar 'yan Jahiliyya, waɗanda ba sa bin wani shugaba, kuma ba sa tarowa zuwa jama'a ɗaya, kawai sun kasance ƙungiyoyi da jama'a-jama'a da sashinsu yana yaƙar sashi. (Annabi) Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa wanda ya yi yaƙi ƙarƙashin tutar da ba a fayyace gaskiyarta daga ƙaryarta ba, yana fushi saboda tsantsar ƙanilanci ga mutanensa ko ƙabilarsa, ba don taimakon Addini ko gaskiya ba, sai ya yi yaƙi don ƙabilanci ba tare da basira ko ilimi ba, to, idan aka kasheshi a kan wannan halin, ya zama kamar kisan Jahiliyya. Kuma wanda ya yi fito na fito da al'ummarsa (Annabi) - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yake dukan mutumin kirkinta da fajirinta, ba ya kulawa da abin da yake aikatawa kuma ba ya jin tsoron uƙubarsa na kashe mumininta, kuma ba ya cika alƙawari ga ma'abota alƙawari daga cikin kafirai ko majiɓinta al'amura sai dai ma yana warwaresu, to, wannan yana daga manyan zunubai, wanda ya aikata shi, to, haƙiƙa ya cancanci wannan narkon mai tsanani.

Fa'idoji

  • Biyayya ga shugabanni wajiba ce a abinda ba saɓon Allah ba.
  • A cikinsa akwai gargaɗi mai tsanani ga wanda ya fita daga biyayyar shugaba, kuma ya rabu da jama'ar musulmai, idan ya mutu a kan wannan halin, to, ya mutu a kan tafarkin ma'abota Jahiliyya.
  • A cikin Hadisin akwai hani game da yaƙi don ƙabilanci.
  • Wajabcin cika alƙawarurra.
  • A cikin biyayya da lazimtar jama'a akwai alheri mai yawa, da aminci da nutsuwa, da gyara halaye.
  • Hani daga kamanceceniya da halayen ma'abota Jahiliyya.
  • Umarni da lazimtar jama'ar musulmai.
Sharhi: العربية

بَيَّنَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ مَن خَرَجَ عن طاعة ولاة الأمور، وفارق جماعة الإسلام المُتَّفِقة على بيعة الإمام، فمات على تلك الحال من المفارقة وعدم الطاعة، مات ميتة أهل جاهلية، الذين كانوا لا يطيعون أميرًا ولا يَنْضَمُّونَ إلى جماعة واحدة، بل كانوا فِرَقًا وعصائب يقاتل بعضهم بعضًا. وأخبر صلى الله عليه وسلم أنَّ مَن قاتل تحت راية لا يَستَبينُ فيها وجه الحق من الباطل، يغضب لمحض التَّعَصُّبِ لقومه أو قبيلته، لا لنصرة الدين والحق، فيقاتل تعصُّبًا بغير بصيرة وعلم، فإذا قُتِل على تلك الحال، كانت كقتلة الجاهلية. وأنَّ مَن خرج على أمته صلى الله عليه وسلم يَضربُ صالحَها، وفاجرَها، ولا يبالي بما يفعله ولا يخاف عقوبتَه مِن قَتْلِ مؤمنِها، ولا يفي لأصحاب العهد من الكفار أو ولاة الأمور بعهدِهم بل يَنقضُها، فهو ليس مني ولست منه.

  • النهي عن التشبه بأحوال أهل الجاهلية.
  • وجوب طاعة ولاة الأمور في غير معصية الله عز وجل.
  • التحذير شديد لمن خرج عن طاعة الإمام، وفارق جماعة المسلمين، فإذا مات على هذه الحال، مات ميتة جاهلية.
  • النهي عن قتال العصبية.
  • وجوب الوفاء بالعهود.
  • في الطاعة ولزوم الجماعة الخير الكثير، والأمن والطمأنينة، وصلاح الأحوال.
  • هذا الوعيد في الحديث يدل على أن هذه الأعمال من كبائر الذنوب.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari