Hadisai

Ku sauƙaƙa kada ku tsananta, ku yi bushara kada ku yi kora

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عن أنس بن مالك رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «يَسِّرُوا وَلَا تُعَسِّرُوا، وَبَشِّرُوا وَلَا تُنَفِّرُوا».

Fassara

Daga Anas Ɗan Malik Allah Ya yarda da shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Ku sauƙaƙa kada ku tsananta, ku yi bushara kada ku yi kora.

Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da umarnin sauƙaƙawa da rangwame wa mutane, da kada a tsananta musu a dukkanin lamura na addini da na rayuwa, wannan kuwa a daidai yadda Allah Ya halatta Ya kuma shar’anta. Kuma yana kwaɗaitarwa a kan bushara da alheri, da rashin korar (kyarar) mutane.

Fa'idoji

  • Wajibin dake kan mumini shi ne ya sanya wa mutane son Allah, ya kwadaitar da su alheri.
  • Ya kamata ga mai kiran mutane zuwa ga Allah ya yi nazari cikin hikima a kan yadda zai isar da saƙon Musulunci zuwa ga mutane.
  • Bushara tana haifar da farin ciki da karɓuwa da nutsuwa da abin da mai Da'awa ya ke gabatarwa ga mutane.
  • Tsanantawa tana haifar da ƙyama da kuma juya baya da sanya shakku a maganar mai Da’awah.
  • Yalwatuwar rahamar Allah ga bayinSa, da cewa Ya yardar musu da addini mai sauƙi da Shari’ah mai rangwame.
  • Sauƙi da aka yi umarni da shi, shi ne wanda Shari’a ta zo da shi.
Sharhi: العربية

يَأمُرُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم بالتخفيف والتيسير على الناس وعدم التَّعْسِيْر عليهم في جميع أمور الدين والدنيا، وذلك في حدود ما أباح الله وشرع. ويَحُثُّ على تَبْشِيرِهم بالخير، وعدم تَنْفِيرِهم منه.

  • واجب المؤمن أن يحبب الناس بالله ويُرغِّبهم في الخير.
  • ينبغي على الداعي إلى الله أن ينظر بحكمة إلى كيفية تبليغ دعوة الإسلام إلى الناس.
  • التبشير يُولِّدُ السرورَ والإقبالَ والاطمئنانَ للداعي ولِمَا يَعرِضه على الناس.
  • التعسير يولِّدُ النفورَ والإدبارَ والتشكيكَ في كلام الداعي.
  • سعة رحمة الله بعباده وأنه رضي لهم دينًا سمحًا وشريعة ميسرة.
  • التيسير المأمور به هو ما جاءت به الشريعة.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari