Hadisai

Ku dinga maimaita wannan Alƙur’anin, ina rantse muku da wanda ran Muhammad yake a hannunSa ya fi saurin kufcewa sama da raƙumin da ya ke a dabaibayi

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عن أبي موسى الأشعري رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «تَعَاهَدُوا هَذَا الْقُرْآنَ، فَوَالَّذِي نَفْسُ مُحَمَّدٍ بِيَدِهِ لَهُوَ أَشَدُّ تَفَلُّتًا مِنَ الْإِبِلِ فِي عُقُلِهَا».

Fassara

Daga Abu Musa Al-ash'ariy Allah Ya yarda da shi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Ku dinga maimaita wannan Alƙur’anin, ina rantse muku da wanda ran Muhammad yake a hannunSa ya fi saurin kufcewa sama da raƙumin da ya ke a dabaibayi.

Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi umarnin yawan maimaita Alƙur’ani da dagewa a kan karanta shi; domin kada a manta bayan an haddace shi a zuciya, [Annabi] tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kuma ƙarfafi hakan da rantsuwa a kan Alƙur’ani ya fi saurin ɓacewa da tafiya daga zuciya a kan raƙumi da aka ɗaure, ga shi a ɗaure da igiya a ƙwauri, idan mutum yana yawan bibiyarsa sai ya riƙeshi, idan kuma ya sakeshi sai ya tafi ya ɓace.

Fa'idoji

  • Idan mahaddacin Alƙur’ani ya dage lokaci bayan Lokaci zai kasance yana nan a haddace a zuciyarsa, idan kuwa ba haka ba sai ya tafi ya manta da shi.
  • Daga cikin fa'idojin bibiyar Alkur’ani akwai: samun lada, da ɗaukakar daraja a ranar Alkiyama.
Sharhi: العربية

أَمَرَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم بمُعاهَدةِ القرآنِ والمواظبةِ على تلاوتِهِ كي لا ينساه بعد أن كان حافظًا له في صدرِهِ، وأَكَّدَ ذلك بِحَلِفِهِ صلى الله عليه وسلم على أنَّ القرآنَ أشدُّ تَخَلُّصًا وذهابًا من الصدور مِن الإبل المَعقولة وهي المشدودة بحبلٍ في وسط الذراع، إنْ تَعاهدَها الإنسانُ أَمْسَكَها وإنْ أَطْلَقَها ذهبتْ وضاعتْ.

  • إنْ واظَبَ حافظُ القرآنِ على تلاوتِه مرَّة بعد مرَّة بقي محفوظًا في قلبه، وإلا ذهبَ عنه ونسيَه.
  • من فوائد تعاهُدِ القرآن: الأجر والثواب، ورفعة الدرجات يوم القيامة.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari