Hadisai

Wanda ya je wurin Ɗan duba (malamin duba) ya tambaye shi wani abu, to, ba za a karɓi Sallarsa ta darare arba’in ba

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عن بعض أزواج النبي صلى الله عليه وسلم عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «مَنْ أَتَى عَرَّافًا فَسَأَلَهُ عَنْ شَيْءٍ لَمْ تُقْبَلْ لَهُ صَلَاةٌ أَرْبَعِينَ لَيْلَةً».

Fassara

Daga wasu cikin matan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: Wanda ya je wurin Ɗan duba (malamin duba) ya tambaye shi wani abu, to, ba za a karɓi Sallarsa ta darare arba’in ba.

Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana tsoratarwa a kan zuwa wurin mai duba -suna ne fitacce na boka, da mai taurari, mai zane a kasa da makamantansu, irin wanda yake kafa dalilin sanin gaibu ta hanyar wasu abubuwa na farko-farkon lamari- zallar tambayarsa a kan wani abu na gaibu, zai haramta masa ladan sallah na kwanaki arba’in, wannan uƙuba ce, a kan wannan laifi, kuma zunubi ne mai girma.

Fa'idoji

  • Haramcin bokanci, da zuwa wurin boka da kuma tambayarsu gaibu.
  • Tabbas ana hanawa mutum ladan biyayya don ya zama uƙuba a gare shi a kan aikata laifi.
  • Yana shiga cikin wannan Hadisin abin ake cewa burji da duba shi, da karanta tafin hannu, da ƙwarya, ko da kuwa leƙawa ne kaɗai, domin duka yana cikin bokanci, kuma yana cikin iƙirarin sanin gaibu.
  • Idan wannan ya zama sakamakon wanda ya je wurin mai duba, to, ya ya halin shi mai duban.??
  • Sallar kwanaki arba’in idan ya yi ba ta yi ba, kuma ba zai rama ta ba, saidai babu ladanta.
Sharhi: العربية

يُحَذِّرُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم من إتيان العرّاف -هو اسم عام للكاهن والمُنِّجم والرَّمَّال ونحوهم، ممن يَسْتَدِلُّ على معرفة الغيب بمقدمات يستعملها -، وأنَّ مُجَرَّدَ سؤالِهِ عن شيء من أمور الغيب سيَحْرِمُه الله به ثوابَ صلاته أربعين يومًا؛ وذلك عقوبة له على هذا الإثم والذنب الكبير.

  • تحريم الكَهَانة، والذهاب إلى الكُهان وسؤالهم عن المغيبات.
  • قد يُحْرَمُ الإنسانُ مِن ثواب الطاعة عقوبة له على فعل المعصية.
  • يَدْخُلُ في الحديث ما يُسمّى بالأبراج والنظر فيها، وقراءة الكَفِّ والفنجان -ولو على سبيل الاطلاع فقط-؛ لأن ذلك كلَّه من الكهانة ومن دعوى علم الغيب.
  • إذا كان هذا جزاءَ مَن أتى العَرّاف، فكيف بجزاء العراف نفسه؟
  • صلاة أربعين يومًا تَقَعُ مُجزئة لا يَجِبُ قضاؤها، ولكن لا ثواب فيها.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari