Hadisai

Ku ciyar da mayunwaci, ku duba mara lafiya, ku fanso wanda aka ribace

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي مُوسَى الأَشْعَرِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «أَطْعِمُوا الجَائِعَ، وَعُودُوا المَرِيضَ، وَفُكُّوا العَانِيَ».

Fassara

Daga Abu Musa al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ku ciyar da mayunwaci, ku duba mara lafiya, ku fanso wanda aka ribace».

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa daga cikin haƙƙin musulmi akan ɗan uwansa musulmi shi ne ya ciyar da mayunwaci, ya ziyarci mara lafiya, ya fanso wanda aka ribace.

Fa'idoji

  • Kwaɗaitarwa akan taimakekeniya tsakanin musulmai.
  • Kwaɗaitarwa akan ciyar da mayunwaci mai buƙatar cin abinci, to wannan an yi umarni a ciyar da shi.
  • Halaccin gaida mara lafiya; dan rage masa raɗaɗi, da yi masa addu'a, da samun lada, da wanin haka.
  • Kwaɗaitarwa akan fansar wanda aka ribace idan kafirai sun ribace shi, hakan ko dai bada biyan wani abuba dan tsamo shi daga cikinsu, ko ta hanyar musayar fursuna kafiri daga cikin waɗanda aka ribato; wato: Ta hanyar musaya.
Sharhi: العربية

بيَّن النبي صلى الله عليه وسلم أن من حق المسلم على أخيه المسلم أن يطعم الجائع، ويزور المريض، ويفك الأسير.

  • الحث على التعاون بين المسلمين.
  • الحث على إطعام الجائع المحتاج إلى الطعام، فهذا مأمورٌ بإطعامه.
  • مشروعية العيادة للمريض؛ جبرًا لخاطره، والدعاء له، وحصول الأجر، وغير ذلك.
  • الحرص على فك الأسير إذا أسَره الكفار، وذلك إما بدفع مقابل لتخليصه منهم، أو بمقابلته بمأسور من الكفار، أي: على سبيل المبادلة.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari