Hadisai

Wanda ya kashe kafirin amana ba zai ji ƙamshin aljanna ba, kuma ƙamshinta ana samunsa daga (tsawon) tafiyar shekara arba'in

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عن عبد الله بن عمرو رضي الله عنهما عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «مَنْ قَتَلَ مُعَاهَدًا ‌لَمْ ‌يَرَحْ ‌رَائِحَةَ الْجَنَّةِ، وَإِنَّ رِيحَهَا تُوجَدُ مِنْ مَسِيرَةِ أَرْبَعِينَ عَامًا».

Fassara

Daga Abdullahi Ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya kashe kafirin amana ba zai ji ƙamshin aljanna ba, kuma ƙamshinta ana samunsa daga (tsawon) tafiyar shekara arba'in".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana narko mai tsanani a kan wanda ya kashe kafirin amana - shi ne kafiri wanda ya shiga garin musulunci bisa alƙawari da amincin - cewa ba zai shaƙi ƙamshin aljanna ba, kuma ƙamshinta yana kasancewa ne a kan nisan tafiyar shekara arba'in.

Fa'idoji

  • Haramcin kashe kafirin amana da zimmi da musta'aman (wanda aka ba shi amincin ɗan wani lokaci) daga kafirai, kuma cewa hakan babban laifi ne daga manyan laifuka.
  • Kafirin amana: Shi ne wanda aka yi alƙawari da shi daga kafirai a kan ya zauna a garinsa ba zai yaƙi musulamai ba su ma ba za su yaƙe shi ba. Zimmi kuma: Shi ne wanda ya zauna a garin musulmai ya ba da jizya. Musta'aman kuma: Shi ne wanda ya shiga garin musulmai a kan alkawari da aminci na wani ƙayyadajjen lokaci.
  • Gargaɗi daga ha'intar alƙawurra (da aka ƙulla) tare da wanin musulmai.
Sharhi: العربية

يُبَيِّنُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم الوعيدَ الشديدَ على أنَّ مَن قَتَلَ مُعاهَدًا -وهو مَن دخل من الكفار إلى دار الإسلام بِعَهْدٍ وأمان- بأنه لن يَشمَّ رائحةَ الجنة، وإنَّ ريحَها يكون على بُعدِ مسيرة أربعين عامًا.

  • تحريم قتل المُعاهَد والذِّمِّي والمُستأمَن من الكفار، وأنه كبيرة من كبائر الذنوب.
  • المعاهد: هو مَن أُخِذَ عليه العهد من الكفار وهو يقيم في بلاده لا يحارب المسلمين ولايحاربونه، والذِّمِّي: هو من استوطن دارَ المسلمين ودفع الجزية، والمستأمَن: هو مَن دخل دار المسلمين بعهد وأمان لوقت محدد.
  • التحذير من خيانة العهود مع غير المسلمين.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari