Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضيَ اللهُ عنهُما أَنَّ رَسُولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم: نَهَى عَنْ كُلِّ ذِي نَابٍ مِنَ السِّبَاعِ، وَعَنْ كُلِّ ذِي مِخْلَبٍ مِنَ الطَّيْرِ.
Fassara
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Ya yi hani daga dukkan mai fika daga zakoka, da kuma dukkan mai akaifa daga tsuntsaye.
Sharhi
Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani daga cin dukkan zakuna daga dabbobin masu farauta waɗanda suke farauta ta hanyar hakoransu, da kuma cin dukkan tsuntsun da yake yankewa kuma yake kamu da faratansa.
Fa'idoji
- Kwaɗayin musulunci akan abubuwa tsarkaka na halas a cikin kowane abu daga abubuwan ci da abubuwan sha da wasunsu.
- Asali, a cikin abubuwan ci shi ne halacci; sai abinda dalili ya yi nuni akan haramcinsa.
Sharhi: العربية
نَهَى النبيُّ صلى الله عليه وسلم عن أكْلِ كلِّ سَبُعٍ من الحيوانات المُفْتَرِسَة التي تَصِيْد بواسطة نابِها، وعن أَكْلِ كلِّ طَيْرٍ يَقْطَع ويُمْسِكُ بمِخْلَبِهِ.
- حرص الإسلام على الطيِّبات في كل شيء من المأكل والمشرب وغيرها.
- الأصل في الأطعمة الحِلّ؛ إلا ما دلَّ الدليل على تحريمه.