Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «يَقْبِضُ اللَّهُ الأَرْضَ، وَيَطْوِي السَّمَوَاتِ بِيَمِينِهِ، ثُمَّ يَقُولُ: أَنَا المَلِكُ، أَيْنَ مُلُوكُ الأَرْضِ».
Fassara
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Allah Zai damke kasa, Zai ninke sammai da hannunSa na dama, sannan Ya ce: Ni ne sarki, ina sarakunan kasa".
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Madaukakin sarki - a ranar Alkiyama Zai damke kasa Ya tattarota, Ya ninke sama da hannunSa na dama Ya ninke sashinta a saman sashi Ya tafiyar da ita Ya karar da ita, sannan Ya ce: Ni ne sarki, ina sarakunan kasa?!
Fa'idoji
- Tinatarwa da cewa mulkin Allah Shi ne wanzajje kuma mulkin waninSa mai gushewa ne.
- Girman Allah da girman ikonSa da sarautarSa da cikar mulkinSa.
Sharhi: العربية
أَخْبَرَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ الله تعالى يوم القيامة يقبض الأرضَ ويجمعُها، ويَطوي السماءَ بيمينه ويلفّ بعضَها فوق بعض ويذهب بها ويفنيها، ثم يقول: أنا المَلك، أين ملوك الأرض؟!
- التذكير بأنَّ مُلْكَ الله هو الباقي ومُلْكُ غيرِه زائل.
- جلال الله وعظمة قدرته وسلطانه وتمام ملكه.