Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ أَسْمَاءَ بِنْتِ أَبِي بَكْرٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا، قَالَتْ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنِّي عَلَى الحَوْضِ حَتَّى أَنْظُرَ مَنْ يَرِدُ عَلَيَّ مِنْكُمْ، وَسَيُؤْخَذُ نَاسٌ دُونِي، فَأَقُولُ: يَا رَبِّ مِنِّي وَمِنْ أُمَّتِي، فَيُقَالُ: هَلْ شَعَرْتَ مَا عَمِلُوا بَعْدَكَ، وَاللَّهِ مَا بَرِحُوا يَرْجِعُونَ عَلَى أَعْقَابِهِمْ».
Fassara
Daga Asma'u bint AbuBakar - Allah Ya yarda da su - ta ce : Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai ni ina kan tafkina har in kalli wanda zai zo ya iso daga cikinku, za'a rike wasu mutane a kusa da ni, sai in ce: Ya Ubangiji daga gareni ne daga al'ummata ne, sai a ce: Shin ka san abinda suka aikata a bayanka, wallahi ba su gushe ba suna komawa akan digadigensu".
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa shi zai kasance a ranar Alkiyama akan tafkinsa dan ya ga wanda zai zo daga al'ummarsa zuwa tafkin, Kuma za'a rike wasu mutane a kusa da shi - aminci ya tabbata agare shi - sai ya ce: Ya Ubangiji daga gareni ne kuma daga al'ummata ne, Sai a ce: Shin ka san abinda suka aikata bayan rabuwarka da su, wallahi ba su gushe ba suna komawa akan bayansu suna yin ridda daga addininsu, su ba sa tare da kai, kuma ba sa cikin al'ummarka.
Fa'idoji
- Rahamar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga al'ummarsa da kuma kwadayinsa gare su .
- Hadarin sabawa abinda (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake akansa.
- Kwadaitarwa akan riko da sunnar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Sharhi: العربية
يُبيِّن النبي صلى الله عليه وسلم بأنَّه سيكون يوم القيامة على حوضه لينظُرَ مَن يأتي مِن أمَّته إلى الحوض، وسَيُؤخَذ ناسٌ بالقرب منه عليه الصَّلاة والسلام فيقول: يا رب منّي ومِن أُمَّتي، فيُقال: هل عَلِمْت ما عملوا بعد مفارقتهم إيّاك، والله ما زالوا يرجعون على أدبارِهم ويرتَدُّون عن دينِهم، فلا هم مِنك، ولا مِن أمَّتِك.
- رحمة النبي صلى الله عليه وسلم بأمته وحرصه عليهم.
- خطورة مخالفة ما كان عليه النبي صلى الله عليه وسلم.
- الحث على التمسك بسنة النبي صلى الله عليه وسلم.