Hadisai

Shin dayanku yana son idan ya koma zuwa iyalansa ya samu manyan taguwowi masu ciki masu giba?

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ ‌أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَيُحِبُّ أَحَدُكُمْ إِذَا رَجَعَ إِلَى أَهْلِهِ أَنْ يَجِدَ فِيهِ ثَلَاثَ خَلِفَاتٍ عِظَامٍ سِمَانٍ؟» قُلْنَا: نَعَمْ. قَالَ: «فَثَلَاثُ آيَاتٍ يَقْرَأُ بِهِنَّ أَحَدُكُمْ فِي صَلَاتِهِ خَيْرٌ لَهُ مِنْ ثَلَاثِ خَلِفَاتٍ عِظَامٍ سِمَانٍ».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shin dayanku yana son idan ya koma zuwa iyalansa ya samu manyan taguwowi masu ciki masu giba?" muka ce: Eh. Ya ce; "To ayoyi uku dayanku zai karantasu a cikin sallarsa sun fiye masa alheri daga taguwowi uku manya masu ciki".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa ladan karanta ayoyi uku a cikin sallah; shi ne mafi alheri daga mutum ya sami taguwowi uku masu ciki manya a cikin gidansa.

Fa'idoji

  • Bayanin falalar karanta Alkur’ani a cikin sallah.
  • Ayyuka na gari su ne mafi alheri kuma mafi wanzuwa daga jin dadin duniya mai karewa.
  • Wannan falalar ba ababen kayyadewa bane da karanta ayoyi uku kawai; duk lokacin da mai sallah ya kara karanta ayoyi a cikin sallarsa ladanta zai zama mafi alheri gare shi daga adadinsu daga taguwowi masu ciki.
Sharhi: العربية

يُبَيِّن النبي صلى الله عليه وسلم أن أجر قراءة ثلاثة آيات في الصلاة؛ خير من أن يجد الإنسان في بيته ثلاث نُوْقٍ حوامل عظام سمان.

  • بيان فضل قراءة القرآن في الصلاة.
  • الأعمال الصالحة خير وأبقى من متاع الدنيا الفاني.
  • هذا الفضل ليس مُقيَّدًا بقراءة ثلاث آيات فقط؛ فكلما زاد المصلي من قراءة الآيات في صلاته كان ثوابها خيرًا له من عددهن من الخَلِفات.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari