Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ: أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ افْتَقَدَ ثَابِتَ بْنَ قَيْسٍ، فَقَالَ رَجُلٌ: يَا رَسُولَ اللهِ، أَنَا أَعْلَمُ لَكَ عِلْمَهُ، فَأَتَاهُ فَوَجَدَهُ جَالِسًا فِي بَيْتِهِ، مُنَكِّسًا رَأْسَهُ، فَقَالَ: مَا شَأْنُكَ؟ فَقَالَ شَرٌّ، كَانَ يَرْفَعُ صَوْتَهُ فَوْقَ صَوْتِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَدْ حَبِطَ عَمَلُهُ، وَهُوَ مِنْ أَهْلِ النَّارِ، فَأَتَى الرَّجُلُ فَأَخْبَرَهُ أَنَّهُ قَالَ كَذَا وَكَذَا، فَرَجَعَ الْمَرَّةَ الْآخِرَةَ بِبِشَارَةٍ عَظِيمَةٍ، فَقَالَ: «اذْهَبْ إِلَيْهِ فَقُلْ لَهُ: إِنَّكَ لَسْتَ مِنْ أَهْلِ النَّارِ، وَلَكِنْ مِنْ أَهْلِ الْجَنَّةِ».
Fassara
Daga Anas Ɗan Malik Allah Ya yarda da shi Lallai Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya nemiSabitu ɗan Ƙais (domin bai ganshi ba) sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah, ni zan samo maka labarinsa, sai ya zo masa sai ya same shi a zaune a gidansa ya sunkuyar da kansa, sai ya ce: Meke damunka? sai ya ce: Sharri, ya kasance yana ɗaga sautinsa sama da sautin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, to, haƙiƙa aikinsa ya ɓaci, kuma shi yana daga 'yan wuta. Sai mutumin ya zo sai ya ba shi labarin cewa kaza da kaza, sai ya dawo a karo na ƙarshe da babban albishir, sai ya ce: "Ka tafi zuwa gareshi ka ce masa: Lallai kai ba ka cikin 'yan wuta, sai dai kana daga cikin 'yan aljanna".
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya rasa Sabitu Dan Ƙais - Allah Ya yarda da shi - ya yi tambaya game da shi (ya yi cigiyarsa), sai wani mutum ya ce: Ni zan samo maka labarinsa, da dalilin fakuwarsa, sai ya tafi wurinsa sai ya same shi yana cikin baƙin ciki yana mai sunkuyar da kansa a gidansa, sai ya tambaye shi : Meke damunka? sai Sabitu ya ba shi labarin abin da ke tare da shi na sharri; domin cewa ya kasance yana ɗaga sautinsa sama da sautin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kuma haƙiƙa Allah Ya yi alkawarin narko daga aikata hakan da ɓacin aikinsa, kuma cewa shi yana daga 'yan wuta! Sai mutumin ya dawo zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya sanar da shi da hakan, sai Annabi - tsaira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya umarce shi ya koma wa Sabitu ɗan Ƙais ya yi masa albishir da cewa shi ba ya daga 'yan wuta, sai dai yana daga 'yan aljanna, domin cewa ya kasance mai babbar murya ne a halitta, domin shi ya kasance mai huɗubar Manzon Allah ne - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -. kuma mai yi wa mutanen Madina huɗuba.
Fa'idoji
- Bayanin falalar Sabitu ɗan Ƙais - Allah Ya yarda da shi - kuma cewa shi yana daga cikin 'yan aljanna.
- Damuwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da sahabbai da bibiyarsa garesu.
- Tsoron sahabbai - Allah Ya yarda da su - game da ɓacin aikinsu.
- Wajabcin ladabi wajen yi masa magana - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a rayuwarsa, da ƙanƙan da muryoyi a lokacin jin sunnarsa bayan ya rasu.
Sharhi: العربية
افتَقَدَ النَّبيُّ صلَّى اللهُ عليه وسلَّمَ ثابتَ بن قيس رضي الله عنه وسَألَ عنه، فقال رَجلٌ: أنا أَجِدُ لك خَبرَه، وسببَ تغيُّبِه، فذهَبَ إليه فوجَدَه حَزينًا مُطرقاً رَأسَه في بَيتِه، فسَأَلَه: ما شأنُكَ؟ فأخبَرَه ثابتٌ ما به مِن الشَّرِّ؛ لأنَّه كان يَرفَعُ صَوْتَه فوقَ صَوتِ النَّبيِّ صلَّى اللهُ عليه وسلَّمَ، وقدْ تَوعَّدَ اللهُ من فعل ذلك ببطلان عمَلِه، وأنه من أهل النار! فرجَع الرَّجلُ إلى النَّبيِّ صلَّى اللهُ عليه وسلَّمَ وأخبَرَه بذلك، فأمَرَه النَّبيُّ صلَّى اللهُ عليه وسلَّمَ أنْ يَرجِعَ إلى ثابتٍ ويبشِّره بأنَّه ليس مِن أهلِ النَّارِ ولكن من أهلِ الجَنَّةِ، وذلك لأنَّ صَوتَه كان مُرتفِعًا خِلْقةً، ولأنَّه كان خَطيبَ رَسولِ اللهِ صلَّى اللهُ عليه وسلَّمَ، وخَطيبَ الأنْصارِ.
- بيان فضل ثابت بن قيس رضي الله عنه وأنّه مِن أهل الجنة.
- اهتمام النبي صلى الله عليه وسلم بالصحابة وتفقُّده لهم.
- خشية الصحابة رضوان الله عليهم وخوفهم مِن أن تُحْبَطَ أعمالُهم.
- وجوب الأدب في خِطابِه صلى الله عليه وسلم في حياتِه، وخفض الأصوات عند سماع سُنّتِه بعد وفاته.