Hadisai

Na ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi fitsari, sannan ya yi alwala kuma ya yi shafa akan huffinsa

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ إِبرَاهِيمَ النَّخَعِيِّ عَنْ هَمَّامِ بنِ الحَارِثِ قَالَ: بَالَ جَرِيرٌ، ثُمَّ تَوَضَّأَ، وَمَسَحَ عَلَى خُفَّيْهِ، فَقِيلَ: تَفْعَلُ هَذَا؟ فَقَالَ: نَعَمْ، رَأَيْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بَالَ، ثُمَّ تَوَضَّأَ وَمَسَحَ عَلَى خُفَّيْهِ. قَالَ الأَعْمَشُ: قَالَ إِبْرَاهِيمُ: كَانَ يُعْجِبُهُمْ هَذَا الحَدِيثُ؛ لِأَنَّ إِسْلَامَ جَرِيرٍ، كَانَ بَعْدَ نُزُولِ المَائِدَةِ.

Fassara

Daga Ibrahim al-Nakha'i daga Hammam Ibnul Haris ya ce: Jarir ya yi fitsari, sannan ya yi alwala ya yi shafa akan huffinsa, sai aka ce: Ya kake yin haka? ya ce: Eh, Na ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi fitsari, sannan ya yi alwala kuma ya yi shafa akan huffinsa. Al-A'amash ya ce: Ibrahim ya ce: Wannan hadisin yana ƙayatar da su; domin musuluntar Jarir, ta kasance ne bayan saukar (Suratul) Ma'idah.

Sharhi

Jarir Ibnu Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - ya yi fitsari sannan ya yi alwala, kuma hakan ya wadatar da yin shafa akan huffinsa bai wanke ƙafafunsa ba, sai wanda ke gefensa Ya ce masa: Ya kake aikata haka?! sai ya ce: Eh, na ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi fitsari, sannan ya yi alwala kuma ya yi shafa akan huffinsa. Jarir ya kasance ya musulunta daga baya-baya, bayan saukar Suratul Ma'idah wacce a cikinta ne ayar alwala take, yana mai nuni da hakan zuwa ga shafa akan huffi ba'a shafe hukuncin sa ba a wannan ayar.

Fa'idoji

  • Kwaɗayin sahabbai da tabi'ai akan bin sunnar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  • Nawawi ya ce: Dukkanin waɗanda ake la'akari da su a cikin Ijma'i sun yi Ijma'i akan halaccin shafa akan huffi a halin tafiya da zaman gida, daidai ne hakan ya kasance dan wata buƙata ne ko dan waninta, haka ma ya halatta ga macen da ta lazimci gidanta da kuma mai cutar shama jika wanda ba ya iya tafiya.
  • Falalar Jarir Ibu Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - yadda ya zama mai yalwar ƙirji, yana jure inkarin ɗalibansa a kansa, koda sun kasance masu kuskure ne.
  • Raddi akan wanda ya yi inkarin shafa akan huffi kuma ya yi da'awar cewa shi an shafe hukuncin; domin cewa hadisin Jarir - Allah Ya yarda shi - ya yi jinkiri akan ayar alwala.
  • Bayanin cewa yana kamata ga wanda wani ya yi masa inkari, kuma ya kasance yana ƙudirce ingancinsa cewa kada ya yi fushi akan wanda ya yi masa inkari, kuma ya tattauna da shi gwargwadan zatansa, kai ya bayyanar masa madogararsa a kan hakan da abin da yake mafi kyau.
  • Kafa hujja da tarihi a lokacin buƙatuwa zuwa gare shi .
Sharhi: العربية

بال جرير بن عبد الله رضي الله عنه ثم توضأ، واكتفى بالمسح على خُفَّيه ولم يغسل رجليه، فقال له مَن حوله: تفعل هذا؟! فقال: نعم، رأيت النبي صلى الله عليه وسلم بال، ثم توضأ ومسح على خفيه. وكان جرير قد أسلم متأخِّرًا بعد نزول سورة المائدة التي فيها آية الوضوء، مشيرًا بذلك إلى أن المسح على الخفين لم يُنسخ بتلك الآية.

  • حرص الصحابة والتابعين على اتباع سنة النبي صلى الله عليه وسلم.
  • قال النووي: أجمع من يُعتدُّ به في الإجماع على جواز المسح على الخفين، في السفر والحضر، سواء كان لحاجة أو لغيرها، حتى يجوز للمرأة الملازمة بيتها والزَّمِن الذي لا يمشي.
  • فضل جرير بن عبد الله رضي الله عنه حيث كان واسع الصدر، يتحمل إنكار طلابه عليه، وإن كانوا مخطئين في ذلك.
  • الرد على من أنكر المسح على الخفين وادعى بأنه منسوخ؛ لأن حديث جرير رضي الله عنه متأخر عن آية الوضوء.
  • بيان أنه ينبغي لمن أنكر عليه شيء، وكان يعتقد صحته ألَّا يغضب على من ينكر عليه، ويناقشه بحسب ظنه، بل يبين له مستنده في ذلك بالتي هي أحسن.
  • الاستدلال بالتاريخ عند الحاجة إليه.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari