Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ عُبَيْدِ اللَّهِ بْنِ عَدِيِّ بْنِ الخِيَارِ قَالَ: أَخْبَرَنِي رَجُلَانِ أَنَّهُمَا أَتَيَا النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي حَجَّةِ الوَدَاعِ وَهُوَ يُقَسِّمُ الصَّدَقَةَ، فَسَأَلَاهُ مِنْهَا، فَرَفَّعَ فِينَا البَصَرَ وَخَفَّضَهُ، فَرَآنَا جَلْدَيْنِ، فَقَالَ: «إِنَّ شِئْتُمَا أَعْطَيْتُكُمَا، وَلَا حَظَّ فِيهَا لِغَنِيٍّ، وَلَا لِقَوِيٍّ مُكْتَسِبٍ».
Fassara
Daga Ubaidullahi Ibnu Adi Ibnul Khiyar ya ce: Wasu mutane biyu sun bani labarin cewa sun zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a Hajjin ban kwana alhali shi yana raba sadaka (zakka), sai suka tambaye shi zakkar, sai ya ɗaga idanuwansa garemu ya kuma yi ƙasa da su, sai ya ganmu ƙarfafa ne, sai ya ce: «Idan kun so zan baku ita, babu rabo a cikinta ga mawadaci, ko ƙaƙƙarfan da yake iya neman na kansa».
Sharhi
Wasu mutane biyu sun zo wajen Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a Hajjin ban kwana, alhali shi yana raba sadaka (zakka), kuma suka nemi ya basu daga cikin zakkar, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya sake kallonsu, dan ya gane halinsu, kuma shin ya halatta a basu sadakar ko a'a? Sai ya gansu mazaje ne biyu ƙarfafa, sai ya ce: Idan kuna so zan baku daga cikin zakkar, babu rabo a cikinta ga wanda yake da dukiyar da zata ishe shi, ko ga wanda yake da ikon yin aiki ko juya dukiya, ko da ba shi da dukiyar da za'a ɗauke shi (a matsayin) mawadaci da ita.
Fa'idoji
- Haramcin roƙo ga mutum mawadaci ko ƙaƙƙarfan da zai iya neman na-kansa.
- Asali ga wanda ba’a san yana da dukiyaba to talaka ne da kuma cancantar karɓar sadaka.
- Mujarradin ƙarfi ba ya hukunta rashin cancantar karɓar sadaka, kai babu makawa da a haɗa da iko akan iya nema.
- Mai iko akan neman abin da zai ishe shi ba ya halatta ya karɓi sadaka ta wajibi (wato Zakkah); dan wadatuwarsa da neman na kansa, kamar wadatuwar mawadaci ne da dukiya.
- Tarbiyyar Annabi mai girma ga mutum musulmi akan kamewa, da kuma bayarwa banda karɓa da roƙo da kuma kasala.
Sharhi: العربية
جاء رجلان إلى النبي صلى الله عليه وسلم في حجة الوداع، وهو يقسم الصدقة، وطلبا أن يعطيهما منها، فجعل صلى الله عليه وسلم يكرر النظر إليهما، ليعرف حالهما، وهل تحِلَّ لهما الصدقة، أم لا؟ فرآهما رجلين قويين، فقال: إن أردتما أعطيتكما من الصدقة، ولا نصيب فيها لمن معه مال يكفيه، ولا لقادر على السعي وكسب المال، وإن لم يكن له معه مال يعد به غنيًا.
- تحريم مسألة الشخص الغني أو القوي المكتسب.
- الأصل فيمن لم يعلم له مال الفقر والاستحقاق من الصدقة.
- مجرد القوة لا تقتضي عدم استحقاق الصدقة، بل لا بد من أن ينضم إليها القدرة على الاكتساب.
- القادر على اكتساب ما يكفيه لا يجوز له الأخذ من الصدقة المفروضة؛ لاستغنائه بالكسب، كاستغناء الغني بالمال.
- التربية النبوية العظيمة للشخصية المسلمة على عزة النفس، وعلى العطاء لا الأخذ والسؤال والكسل.