Hadisai

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai taɓa yaƙar wasu mutane ba har sai ya kirasu (zuwa ga Addini)

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neAhmad da Baihaki suka Rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللهُ عَنْهُمَا قَالَ: مَا قَاتَلَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَوْمًا قَطُّ حَتَّى يَدْعُوَهُمْ.

Fassara

Daga Abdullahi Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai taɓa yaƙar wasu mutane ba har sai ya kirasu (zuwa ga Addini).

Sharhi

Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - ya bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai taɓa farawa da yaƙar wasu mutane ba har sai ya kirasu zuwa ga Musulunci a farko, idan ba su amsa kiransa ba sai ya yaƙe su.

Fa'idoji

  • An sharɗanta kira zuwa ga Musulunci kafin yaƙi idan Musuluncin bai isa zuwa garesu ba.
  • Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana kiransu zuwa Musulunci, idan sun ƙi sai ya bijiro musu da bada da jizya, idan sun ƙi sai ya yaƙesu, kamar yadda ya zo a cikin wasu hadisan daban.
  • Hikima a cikin yaƙi ita ce shigar mutane cikin Addinin Musulunci, ba wai kwaɗayi a kan bayinsu ko dukiyoyinsu da garuruwansu ba.
Sharhi: العربية

أخبر ابن عباس رضي الله عنهما أن النبي صلى الله عليه وسلم لم يبدأ بمقاتلة قوم حتى يدعوهم إلى الإسلام أولًا، فإن لم يستجيبوا لدعوته قاتلهم.

  • اشتراط الدعوة إلى الإسلام قبل القتال إذا كان الإسلام لم يبلغهم.
  • كان النبي صلى الله عليه وسلم يدعوهم إلى الإسلام، فإن رفضوا عرض عليهم دفع الجزية، فإن رفضوا قاتلهم، كما جاء في أحاديث أخرى.
  • الحكمة في الجهاد دخول الناس في الإسلام، وليس الطمع في رقابهم وأموالهم وبلادهم.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari