Hadisai

Lallai ne mafi soyuwar sunayenku a wurin Allah (su ne) Abdullahi da Abdurrahman

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنِ ابْنِ عُمَرَ رَضيَ اللهُ عنهما قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنَّ أَحَبَّ أَسْمَائِكُمْ إِلَى اللهِ عَبْدُ اللهِ وَعَبْدُ الرَّحْمَنِ».

Fassara

Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai ne mafi soyuwar sunayenku a wurin Allah (su ne) Abdullahi da Abdurrahman".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mafi soyuwar sunaye a wurin Allah su ne a ambaci namiji da: Abdullahi, ko: Abdurrahman.

Fa'idoji

  • AlƘurɗubi ya ce: Za'a riskar da waɗannan sunayen a abinda ya kasance tamkarsu, kamar Abdurrahim da Abdulmalik da Abdussamad, kaɗai sun kasance mafi soyuwa zuwa ga Allah ne, domin cewa su sun ƙunshi abinda yake shi ne siffa ta wajibi ga Allah da abinda yake shi ne siffa ga mutum kuma wajibi gare shi, shi ne bauta, sannan aka raɓa bawa zuwa ga Ubangiji, raɓawa ta haƙiƙa sai ta gasgata ɗaiɗaikun waɗannan sunayen kuma suka ɗaukaka da wannan jerin, sai wannan falalar ta tabbata garesu. Waninsa kuma ya ce: Hikima a cikin taƙaituwa akan sunaye biyu cewa a cikin Alƙur'ani raɓa bawa zuwa wani suna daga cikn sunayen Allah - Maɗƙaukakin sarki - bai afkuba banda biyun nan, Allah - Madaukakin sarki - Ya ce: {Lallai cewa shi yayin da bawan Allah ya tsaya yana kiransa}, kuma Ya fada a cikin wata ayar daban: {Kuma bayin Ubangiji Arrahman}, kuma fadinSa - Madaukakin sarki - Yana karfafa shi: {Ka ce ku kira Allah ko ku kira Arrahman}.
Sharhi: العربية

أخبر النبي صلى الله عليه وسلم أن أحب الأسماء إلى الله هي تسمية الذَّكَر: عبدالله، أو: عبدالرحمن.

  • قال القرطبي: يلتحق بهذين الاسمين ما كان مثلهما كعبد الرحيم وعبد الملك وعبد الصمد، وإنما كانت أحب إلى الله، لأنها تضمنت ما هو وصف واجب لله وما هو وصف للإنسان وواجب له وهو العبودية، ثم أضيف العبد إلى الرب إضافة حقيقية فصدَّقت أفراد هذه الأسماء وشرفت بهذا التركيب فحصلت لها هذه الفضيلة، وقال غيره: الحكمة في الاقتصار على الاسمين أنه لم يقع في القرآن إضافة عبد إلى اسم من أسماء الله تعالى غيرهما، قال الله تعالى: {وَأَنَّهُ ‌لَمَّا ‌قَامَ عَبْدُ اللَّهِ يَدْعُوهُ} وقال في آية أخرى: {وَعِبَادُ ‌الرَّحْمَنِ} ويؤيده قوله تعالى: { ‌قُلِ ‌ادْعُوا ‌اللَّهَ أَوِ ادْعُوا الرَّحْمَنَ}.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari