Hadisai

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: Mutum uku zan yi rigirma da su a ranar alƙiyama

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «قَالَ اللَّهُ تَعَالَى: ثَلاَثَةٌ أَنَا خَصْمُهُمْ يَوْمَ القِيَامَةِ: رَجُلٌ أَعْطَى بِي ثُمَّ غَدَرَ، وَرَجُلٌ بَاعَ حُرًّا فَأَكَلَ ثَمَنَهُ، وَرَجُلٌ اسْتَأْجَرَ أَجِيرًا فَاسْتَوْفَى مِنْهُ وَلَمْ يُعْطِهِ أَجْرَهُ».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annbai - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: Mutum uku zan yi rigirma da su a ranar alƙiyama: Mutumin da ya bada amana da sunana sannan ya yi yaudara, da mutumin da ya saida ɗa ya ci kuɗinsa, da mutumin da ya hayi ɗan ƙodago ya cika masa aikinsa amma bai ba shi ladansa ba".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: Nau'i uku na mutane zan yi rigima da su a ranar alƙiyama, duk wanda na zama abokin rigimarsa kuwa zan rinjaye shi: Na farko: Wanda ya rantse da Allah, ya yi alƙawari. sannan ya warware shi ya yi yaudara. Na biyu: Wanda ya saida ɗa akan cewa bawa ne, sai kuma ya ci kuɗinsa ya yi tasarrufi da ƙimarsa. Na uku: Wanda ya dauki ɗan ƙodago dan yin wani aiki, sai ya kammala masa aikin, amma bai biya shi kuɗin aikinsa ba.

Fa'idoji

  • Wannan hadisin yana daga abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yake ruwaito shi daga Ubangijinsa, ana ambatonsa da Hadisi Ƙudsi, ko Ilahi, shi ne wanda lafazinsa da ma'anarsa daga Allah ne, sai dai shi babu keɓance-keɓancen Alkur’ani a cikinsa, waɗanda Alkur’ani ya keɓanta da su daga waninsa, kamar bauta da karanta shi, da yin tsarki (alwala) sabo da shi, da fito na fito(ƙalubalanta) da gajiyarwa, da sauransu.
  • Sindi ya ce: An ce: Ambatan ukun bawai dan keɓancewa ba ne; domin Shi Allah - Maɗaukakin sarki - Mai yin rigima ne da dukkanin azalimi, kai a'a dan tsanantawa ne akan waɗanan ukun.
  • Ibnul Jauzi ya ce: Ɗa bawan Allah ne, duk wanda ya yi masa ta'addanci to mamallakinsa zai yi rigima da shi, wanda Shi ne Allah.
  • Khaɗɗabi ya ce: Bautar da ɗa yana faruwa ne da al'amura biyu: Ya 'yanta shi sannan ya ɓoye hakan ko ya musanta. Na biyu: Yasa shi yi masa hidima akan dole bayan ya 'yanta shi, na farkonsu ya fi su tsanani. Na ce: Hadisin babin ya fi tsanani; domin cewa a cikinsa tare da ɓoye 'yantuwar ko musantawarsa aiki yana hukunta hakan na siyarwa da cin kuɗin, daga haka ne narkon ya zama ya fi tsanani.
Sharhi: العربية

أخبر النبي صلى الله عليه وسلم أن الله تعالى قال: ثلاثة أصناف أنا خصمهم يوم القيامة، ومن كنت خصمَه خصمتُه وغلبتُه: الأول: من أعطى يمينه وحلف بالله، وعاهد عهدًا ثم نقضه وغدر. الثاني: من باع رجلًا حرًّا على أنه عبد فأكل ثمنه وتصرّف بقيمته. الثالث: من استأجر أجيرًا لعمل، فاستوفى منه العمل ولم يعطِه ثمن عمله.

  • هذا الحديث مما يرويه النبي صلى الله عليه وسلم عن ربه، ويسمى بالحديث القدسي أو الإلهي، وهو الذي لفظه ومعناه من الله، غير أنه ليست فيه خصائص القرآن التي امتاز بها عما سواه، من التعبد بتلاوته والطهارة له والتحدي والإعجاز وغير ذلك.
  • قال السندي: قيل: ذكر الثلاثة ليس للتخصيص؛ لأنه تعالى خصْمٌ لجميع الظالمين بل للتشديد على هؤلاء الثلاثة.
  • قال ابن الجوزي: الحر عبد الله، فمن جنى عليه فخصمه سيده، الذي هو الله.
  • قال الخطابي: اعتباد الحر يقع بأمرين: أن يعتقه ثم يكتم ذلك أو يجحد. والثاني أن يستخدمه كرهًا بعد العتق، والأول أشدهما. قلت: وحديث الباب أشد؛ لأن فيه مع كتم العتق أو جحده العمل بمقتضى ذلك من البيع وأكل الثمن فمن ثم كان الوعيد عليه أشد.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari