Hadisai

‌Mumini ba zai gusheba a cikin yalwar Addininsa ba, muddin dai bai zubar da jinin da aka haramta masa ba

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنِ ابْنِ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَنْ يَزَالَ المُؤْمِنُ فِي فُسْحَةٍ مِنْ دِينِهِ، مَا لَمْ يُصِبْ دَمًا حَرَامًا».

Fassara

Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «‌Mumini ba zai gusheba a cikin yalwar Addininsa ba, muddin dai bai zubar da jinin da aka haramta masa ba».

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mumini ba zai gushe ba a cikin yalwar ayyukansa na gari, da fatan samun rahamar Allah da gafararSa da kuma rangwaminSa, har sai idan ya kashe wani mutumin da aka haramta masa kashe shi to haƙiƙa ayyukansa zasu yi masa ƙunci; domin ba zasu iya biyan laifin kisa da kuma zunibinsa mai girma ba.

Fa'idoji

  • Girman kisa ba tare da wani haƙƙi ba da kisa na ganganci, domin yana fitar da mumini daga yalwa a cikin Addini zuwa ƙunci.
  • Jinanen da aka haramta nau'i huɗu ne: 1- Jinin musulmi, shi ne mafi girmansu. 2- Jinin kafirin amana (Zimmi), su ne Yahudawa da Nasara waɗanda aka tabbatar da su akan addininsu a garin Musulunci ta hanyar bada jizya, da zartar da hunce-hukuncen Musulunci a cikinsu. 3- Jinin kafirin da aka yi yarjejeniya da shi (Mu'ahad), sune kafiran da suke a garuruwansu waɗanda a tsakaninmu akwai sulhu cewa ba zamu yaƙesu ba suma ba zasu yaƙemu ba. 4- Jinin kafiri Musta'amani, shi ne kafirin da ake yaƙi da shi wanda tsakaninmu babu alƙawari, sai dai shugaba ko wanda yake mallakar hakan daga mataimakansa ya amintar da shi a lokaci iyakantacce cewa zai shigo garin musulmai.
Sharhi: العربية

أخبر النبي صلى الله عليه وسلم أن المؤمن لا يزال في فسحة وسعة أعماله الصالحة، ورجاء رحمة الله ومغفرته وعفوه، حتى إذا قتل إنسانًا محرَّمٌ قتله فقد ضاقت به أعماله؛ لأنها لا تَفِي بوزر القتل وذنبه العظيم.

  • عظم القتل بغير حق والقتل العمد، فإنه يخرج المؤمن من السعة في الدين إلى الضيق.
  • الدماء المحرمة أربعة أصناف: 1- دم المسلم، وهو أعظمها، 2- دم الذمي، وهم اليهود والنصارى الذين أقروا في دار الإسلام على دينهم بالتزام الجزية، ونفوذ أحكام الإسلام فيهم، 3- دم المعاهد، وهم الكفار في بلادهم الذين بيننا وبينهم صلح لا نحاربهم ولا يحاربوننا، 4- دم المستأمِن، وهو الكافر الحربي ليس بيننا وبينه ذمة ولا عهد، لكننا أمّناه في وقت محدد يدخل بلاد المسلمين مِن ولي الأمر أو مَن يملك ذلك من نوَّابه.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari