Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَن أَبي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «لاَ يُشِيرُ أَحَدُكُمْ عَلَى أَخِيهِ بِالسِّلاَحِ، فَإِنَّهُ لاَ يَدْرِي، لَعَلَّ الشَّيْطَانَ يَنْزِعُ فِي يَدِهِ، فَيَقَعُ فِي حُفْرَةٍ مِنَ النَّارِ».
Fassara
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Kada ɗayanku ya yi nuni zuwa ga ɗan uwansa da makami, domin shi bai sani ba wataƙila Shaiɗan ya fizge daga hannunsa sai ya faɗa ciki ramin wuta».
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi ga musulmi ya nuna ɗan uwansa musulmi da kowane irin makami, domin cewa shi bai sani ba wataƙila Shaiɗan ya ɗauke shi akan motsa makamin a hannunsa, sai ya kashe ɗan uwansa ko ya cutar da shi, sai ya faɗa cikin saɓon da zai kai shi ya faɗa cikin ramin wuta.
Fa'idoji
- Bayanin haramcin jinin musulmi.
- Wajabcin girmama musulmi da kiyayewa daga sadar da sharri gare shi ta hanyar aiki ne ko magana, daga hakan akwai nuni da ƙarfe ko da da wasa ne; domin cewa Shaiɗan zai iya zaburar da hannunsa sai ya ƙawata masa dukan ɗan uwansa, ko ya fizge makamin daga hannunsa sai ya faɗa ba tare da zaɓinsa ba sai ya cutar da ɗan uwansa.
- Toshe kafa da yin hani daga abinda zai kai zuwa abinda aka haramta.
- Kwaɗayi akan zaman lafiyar zamantakewar jama'a da kiyaye alaƙoƙi tsakanin mutane, da rashin tsoratasu koda da nuni ne da kuma yi musu tsawa.
Sharhi: العربية
حذر النبي صلى الله عليه وسلم أن يشير المسلم على أخيه المسلم بأي نوع من أنواع السلاح، فإنه لا يعلم لعل الشيطان يحمله على تحريك السلاح في يده، فيقتل أخاه أو يؤذيه، فيقع في المعصية التي تفضي به إلى أن يقع في حفرة من النار.
- بيان حرمة دم المسلم.
- وجوب احترام المسلم والحذر من إيصال الشر إليه بالفعل أو القول، ومن ذلك الإشارة بالحديدة أو بالسلاح، ولو مازحًا؛ لأن الشيطان قد ينزغ بيده ويزين له ضرب أخيه، أو ينزع السلاح من يده فيقع من غير اختياره فيضر أخاه.
- سد الذرائع بالنهي عما يفضي إلى المحظور.
- الحرص على سلامة المجتمع وحفظ العلاقات بين الناس، وعدم تخويفهم وترويعهم ولو بالإشارة والتهديد.