Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: مَا خَطَبَنَا نَبِيُّ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِلَّا قَالَ: «لَا إِيمَانَ لِمَنْ لَا أَمَانَةَ لَهُ، وَلَا دِينَ لِمَنْ لَا عَهْدَ لَهُ».
Fassara
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai taɓayi mana wata huɗuba ba sai ya ce: «Babu imani ga wanda ba shi da amana, kuma babu Addini ga wanda ba shi da alƙawari».
Sharhi
Anas ɗan malik - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa da wahala Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi huɗuba ko ya yi wa'azi sai ya ambaci al'amura biyu: Na farko: Babu imani cikakke ga wanda a ransa akwai ha'inci ga wani mutum a cikin dukiyarsa ko ransa ko kuma iyalansa. Na biyu: Babu Addini cikakke ga wanda yake ha'intar alƙawurra kuma yake warwaresu.
Fa'idoji
- Kwaɗaitarwa akan mayar da amana da kuma cika alƙawari, domin warwaresu yana tauye imani.
- Gargaɗarwa akan ha'intar amana da kuma warware alƙawari, kuma cewa hakan yana daga cikin manyan zunubai.
- Hadisin ya ƙunshi kiyaye amana da kuma alƙawarin da ke tsakanin Allah da bawanSa, da kuma wanda ke tsakanin halitta sashinsu da sashi.
Sharhi: العربية
يُخبر أنس بن مالك رضي الله عنه أنه قَلَّ أن يخطب النبي صلى الله عليه وسلم أو يَعِظ إلا ذَكَر أمرين: الأول: لا إيمان كامل لمن كانت في نفسه خيانة لأحد في ماله أو نفسه أو أهله. الثاني: لا دين كامل لمن يَخون العهود والمواثيق وينقضُها.
- الحث على أداء الأمانة والإيفاء بالعهد، فإن نقضهم يُنقِص الإيمان.
- التحذير من خيانة الأمانة ونقض العهد، وأن ذلك من كبائر الذنوب.
- يشمل الحديث المحافظة على الأمانة والعهد الذي بين الله وبين عبده، والذي بين الخلق بعضهم البعض.