Hadisai

Duk wanda ba ya godewa mutane to ba zai godewa Allah ba

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neAbu Daud ne ya ruwaito shi da Kuma Tirmizi da Ahmad

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «لَا يَشْكُرُ اللَّهَ مَنْ لَا يَشْكُرُ النَّاسَ»

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annbai - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Duk wanda ba ya godewa mutane to ba zai godewa Allah ba".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa duk wanda a al'adarsa ba ya godewa mutane akan alheri da abu mai kyau da suka yi masa to ba zai godewa Allah ba, hakan dan haduwar al'amura biyun da ɗaya, domin wanda daga cikin ɗabi'arsa da al'adarsa ita ce butulcewa ni'imar mutane da barin gode musu, to al'adarsa zata zama butulcewa ni'imar Allah da kuma kasawa a gode maSa.

Fa'idoji

  • Muhimmancin godewa mutane akan aikin laheri.
  • Mai ni'imtarwa a haƙiƙa shine Allah - Maɗaukakin sarki -, ɗabi'u sabubba ne waɗanda Allah - Maɗaukakin sarki - Yake horesu ga wanda Yake so, saboda haka ne lallai cewa godewa mutane yana daga cikin gode wa Allah - Maɗaukakin sarki -.
  • Godewa mutane akan aikin alherinsu dalili ne akan cikar ɗabi'u.
Sharhi: العربية

أخبر النبي صلى الله عليه وسلم أنه لا يشكر الله عادةً من لا يشكر الناس على المعروف والجميل الذي صنعوه له، وذلك لاتصال أحد الأمرين بالآخر، حيث أن من طبعه وعادته كفران نعمة الناس وترك شكرهم، سيكون من عادته كفر نعمة الله والتقصير في شكره عليها.

  • أهمية شكر الناس على المعروف.
  • المنعم حقيقة هو الله تعالى، والخلق أسباب يسخِّرها الله تعالى لمن يشاء، ولذلك فإنَّ شكر الناس من شكر الله تعالى.
  • شكر الناس على معروفهم دليل على كمال الخلق.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari