Hadisai

Ɗayanku ba zai yi imani ba, har sai ya sowa ɗan uwansa abinda yake sowa kansa

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي حَمْزَةَ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ -خَادِمِ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ- عَنْ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «لاَ يُؤْمِنُ أَحَدُكُمْ، حَتَّى يُحِبَّ لِأَخِيهِ مَا يُحِبُّ لِنَفْسِهِ»

Fassara

Daga Abu Hamza Anas ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - hadimin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ɗayanku ba zai yi imani ba, har sai ya sowa ɗan uwansa abinda yake sowa kansa".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa imani cikakke ba ya tabbata ga wani daga musulmai har sai ya so wa ɗan'uwansa abinda yake sowa kansa na ayyukan ɗa'a da nau'ukan alkairai a addini da rayuwa, kuma ya ki abinda yake ki ga kansa, idan ya ga wata tawaya ga ɗan'uwansa musulmi a addininsa, to ya yi kokari a cikin gyarata, idan ya ga wani alheri a cikinsa to ya daidaita shi ya taimake shi, ya yi masa nasiha a al'amarin Addininsa da duniyarsa.

Fa'idoji

  • Wajabcin so wa mutum ga ɗan'uwansa abinda yake so wa kansa; domin kore imani ga wanda ba ya son abinda yake so ga ɗan'uwansa yana nuni akan wajabcin hakan.
  • 'Yan uwantaka a tafarkin Allah sama take akan 'yan uwantaka ta nasaba, to hakkinta shi ne mafi wajaba.
  • Haramcin dukkan abinda yake kore wannan soyayyar na maganganu da ayyuka, kamar algus da raɗa da hassada da ta'addanci akan ran musulmi ko dukiyarsa ko mutuncinsa.
  • Yin anfani da wasu daga lafuzza masu kwaɗaitarwa akan yin aiki; saboda faɗinsa: "Ga ɗan'uwansa".
  • Karmani - Allah Ya yi masa rahama - ya ce: Kuma yana daga cikin imani ya ki wa ɗan'uwansa abinda yake ki wa kansa na sharri, amma bai ambace shi ba; domin son abu mai lazimtar kin kishiyarsa ne , to hakan ya isu akan barin fadinsa.
Sharhi: العربية

بَيَّنَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنّه لا يَتَحقّق الإيمانُ الكامل لأحدٍ من المسلمين حتى يُحبَّ لأخيه ما يحب لنفسه من الطاعات وأنواع الخيرات في الدين والدنيا، ويكره له ما يكره لنفسه، فإن رأى في أخيه المسلم نقصًا في دينه، اجتهد في إصلاحه، وإنْ رأى فيه خيرًا سدَّده وأعانه، ونصحَه في أمر دينِه أو دنياه.

  • وجوب محبة المرء لأخيه ما يحبُّ لنفسه؛ لأن نفي الإيمان عمن لا يحب لأخيه ما يحب لنفسه يدل على وجوب ذلك.
  • الأُخوّة في الله فوق أخوّة النسب، فحقُّها أوجب.
  • تحريم كل ما ينافي هذه المحبة من الأقوال والأفعال كالغش والغيبة والحسد والعدوان على نفس المسلم أو ماله أو عرضه.
  • استخدام بعض الألفاظ المحفِّزة على الفعل؛ لقوله "لأخيه".
  • قال الكِرْماني رحمه الله: ومن الإيمان أيضًا أنْ يُبغِضَ لأخيه ما يبغض لنفسه من الشر، ولم يذكره؛ لأنَّ حب الشيء مستلزم لبغض نقيضه، فترك التنصيص عليه اكتفاء.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari