Hadisai
SALLAR MASU UZURI
Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
sakamako 7
- 3450
Ya Manzon Allah, Banyi Sallar La'asar ba har rana ta kusa faduwa, sai Annabi ya ce: "na rantse da Allah ban sallace ta ba, sai muka tashi zuwa Buthan, sai yayi Alwala don yin Sallah, Muma mukai Alwala don yin haka, sai mukai Sallah La'asar bayan rana ta fadi, sannan yai sallar Magariba bayan ta.
Ingantacce neBukhari da Muslim suka Rawaito shi - 5207
Na yi tafiya da Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- kuma ya kasance baya wuce raka'a biyu, haka ma Abubakar da Umar da Usman.
Ingantacce neBukhari da Muslim suka Rawaito shi - 5323
Manzon Allah ya Kasance yana hadawa a tafiya tsakanin Azahar da La'asar; idan ya kasance akan abin hawa, kuma yana hadawa tsakanin Magriba da Isha.
Ingantacce neBuhari ne ya rawaito shi - 7187
Annabi ya hada tsakanin Magriba da Isha kuma kowacce daya akwai Iqama, kuma bai yi tasbihi a tsakaninsu sai a karshe daya.
Ingantacce neBukhari da Muslim suka Rawaito shi - 10929
Naga Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yanazaune ya tanqwashe Qafafunsa
Ingantacce neAl-Nasa'i Ya Rawaito shi - 10951
Ka yi Sallah a tsaye, idan ba za ka iya ba, to, a zaune, idan ba za ka iya ba, to, a ɓarin jiki
Ingantacce neBukhari ne ya rawaito shi - 10952
Kayi sallah a Qasa in zaka iya, idan kuma ka kasa to kayi nuni, kasanya Sujadarka Qasaqasa da ruku'unka.
Ingantacce neBazzar ne Ya Rawaito shi - Al-Baihaki ne Ya Rawaito shi