Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عن عمران بن حصين رضي الله عنه قال: كَانَتْ بِي بَوَاسِيرُ، فَسَأَلْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَنِ الصَّلَاةِ، فَقَالَ: «صَلِّ قَائِمًا، فَإِنْ لَمْ تَسْتَطِعْ فَقَاعِدًا، فَإِنْ لَمْ تَسْتَطِعْ فَعَلَى جَنْبٍ».
Fassara
Daga Imaran Ɗan Husain Allah Ya yarda da shi, ya ce: Na kasance Ina da basir, sai na tambayi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi dangane da sallah sai ya ce: Ka yi Sallah a tsaye, idan ba za ka iya ba, to, a zaune, idan ba za ka iya ba, to, a ɓarin jiki.
Sharhi
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayyana asali a Sallah shi ne a yi ta a tsaye, sai idan ba za a iya ba, sai a yi ta a zaune, idan ba zai iya sallar a zaune ba, to, ya samu ya yi a gefen jikinsa.
Fa'idoji
- Sallah ba ta faɗuwa muddin hankali na nan, sai ya kasance daga wannan yanayin, zuwa wancan yanayin gwargwadon damar da yake da ita.
- Sauƙi da rangwamen Musulunci cewa bawa zai aikata ibada yadda yake da iko.
Sharhi: العربية
بَيَّنَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ الأصلَ في الصلاةِ القيامُ، إلّا في حال عدم الاستطاعة فيُصلِّي جالسًا، وإنْ لم يستطع الصلاةَ جالسًا فله أن يُصلِّي على جَنْبِه.
- الصلاة لا تسقط ما دام العقلُ ثابتًا، فيكون الانتقال من حال إلى حال حسب الاستطاعة.
- سماحة ويُسْر الإسلام في أنَّ العبدَ يفعل من العبادة ما يستطيع.