أَرَءَيْتَ ٱلَّذِى يُكَذِّبُ بِٱلدِّينِ
Shin, ka ga wanda ke ƙaryatãwa game da sakamako?
Ku saurara, ku maimaita
Sauraro kawai: wannan naɗin koyarwa ba shi da ingantattun lokutan ayoyi. Maimaitawa tana sake fara surar gaba ɗaya.
Shin, ka ga wanda ke ƙaryatãwa game da sakamako?
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ
أَرَءَيْتَ ٱلَّذِى يُكَذِّبُ بِٱلدِّينِ
Shin, ka ga wanda ke ƙaryatãwa game da sakamako?
فَذَٰلِكَ ٱلَّذِى يَدُعُّ ٱلْيَتِيمَ
To, wan nan shi ne ke tunkure marãya (daga haƙƙinsa).
وَلَا يَحُضُّ عَلَىٰ طَعَامِ ٱلْمِسْكِينِ
Kuma bã ya kwaaitarwa bisa bãyar da abinci ga matalauci.
فَوَيْلٌ لِّلْمُصَلِّينَ
To, bone yã tabbata ga masallata.
ٱلَّذِينَ هُمْ عَن صَلَاتِهِمْ سَاهُونَ
Waɗan da suke masu shagala daga sallar su.
ٱلَّذِينَ هُمْ يُرَآءُونَ
Waɗan da suke yin riya (ga ayyukansu)
وَيَمْنَعُونَ ٱلْمَاعُونَ
Kuma suna hana taimako.
Fassarar Hausa - Abubakar Gumi, bugu na 1.2.2, QuranEnc.com. Ba a canza rubutun da aka wallafa ba.