البقرة

Al-Baƙarah

ayoyi 286MadaniyaJuzu'i 1

Mahmoud Khalil Al-HussaryHafsu daga Asim - Murattal

Saitunan karatu

Jagorar launukan tajwidi

Sunaye, misalai da layukan ƙasa iri-iri suna bayyana ƙa'idojin baya ga launi. An ɗauko misalan daga rubutun Alƙur'ani da aka wallafa.

Gunna
وَمِمَّا2:3
Nau'o'in Ikhfa'i
يُنفِقُونَ2:3
Nau'o'in Idgami
هُدًى لِّلْمُتَّقِينَ2:2
Iƙlabi
أَلِيمٌۢ بِمَا2:10
Ƙalƙala
رَزَقْنَـٰهُمْ2:3
Madda: harka 2
ٱلرَّحْمَـٰنِ1:1
Madda: harka 2, 4 ko 6
ٱلرَّحِيمِ1:1
Madda: harka 4 ko 5
بِمَآ2:4
Madda: harka 6
ٱلضَّآلِّينَ1:7
Hamzatul wasli
ٱللَّهِ1:1
Lam Shamsiyya
ٱلرَّحْمَـٰنِ1:1
Haruffan da ba a furtawa
ٱلصَّلَوٰةَ2:3

Alamomin tajwidi: cpfair/quran-tajweed (CC BY 4.0), an gina su daga ReciteQuran.com da mus'hafan tajwidi na Dar al-Maarifah; an daidaita wurarensu da rubutun Tanzil na yanzu.

Fassarar Hausa - Abubakar Gumi. Siga: 1.2.2. Sabuntawa ta ƙarshe: 2025-06-26. QuranEnc.com

  1. 72

    وَإِذْ قَتَلْتُمْ نَفْسًا فَٱدَّٰرَْٰٔتُمْ فِيهَا ۖ وَٱللَّهُ مُخْرِجٌ مَّا كُنتُمْ تَكْتُمُونَ

    Kuma a lõkacin da kuka yi kisan kai, kuka dinga tunkuɗa wa jũna laifĩ a cikinsa,[1] kuma Allah Mai fitar da abin da kuka kasance kuna ɓõyẽwa ne.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Asalin ƙissar, wani mutum ne mai arziƙi da yawa daga cikin Banĩ Isra'ĩla amma bã shida magaji sai ɗan ɗan'uwan sa. Saboda yayi gãdo, sai ya kashe shi da dare, ya kuma ɗauke shi ya ajiye shi a bakin ƙofar wani mutum, a cikin su. Da safiyã ta wãye, sai suka tãshi dõmin su yi faɗa a tsakãnin dangin wanda aka kashe da dangin wanda aka same shi a ƙofarsu, sa'an nan suka haɗa ra'ayi ga su kai ƙãra ga Manzon Allah, Mũsã. Suka isa gareshi, suka ba shi lãbãrin. Sai yace musu: "Lalle ne, Allah Yã ce: "Ku yanka wata sãniya." Da sun yanke kõwace irin sãniya da buƙãtarsu ta biya musu, amma sai suka yi ta yin tambayoyi ana bã su amsa, kuma yanã ƙãra yi musu wuyã, har suka kai ga a sifantã musu sãniyar yãro mai ɗã'a ga uwarsa wadda aka ce: bã zã a sayar musu da ita ba sai da zĩnãriya cike da fãtarta ko dai dai da nauyinta sau gõma. Bayan sun saye ta suka yanka ta sai Mũsã ya ce musu, su dõki wanda aka kashen nan da wani juzu'i nata. Suka dõke shi da ƙashin ta kõ harshenta, sai ya tãshi ya ce: "Wane ɗan ɗan'uwãna, ya kasheni." Sai suka kãma wanda ya yi kisar suka kashe shi. Tartĩbin Alƙur'ãni ya yi ishara da mas'alar tsaurin kan Banĩ Isra'ila da hikimar bin umurnin Allah, da ĩkon tãyar da matattu da gaskiyar Wahayin Annabawa, da asiran da Allah ke sanyãwa a cikin wasu abũbuwa dõmin su zama sanadi ga aukuwar wasu, da yadda yake azurta mãsu yi masa ɗã'a, da sauran su duk a cikin ƙissa guda, ba da ya ambaci tsarin asalinta ba. Tsarki ya tabbata ga Allah.

    Tafsirin As-Sa'di (Larabci)

    Ya ƙunshi ayoyi 72 - 73

    {72 - 73} فلما ذبحوها قلنا لهم اضربوا القتيل ببعضها، أي: بعضو منها إما بعضو معين أو أي عضو منها فليس في تعيينه فائدة؛ فضربوه ببعضها؛ فأحياه الله، وأخرج ما كانوا يكتمون؛ فأخبر بقاتله، وكان في إحيائه - وهم يشاهدون - ما يدل على إحياء الله الموتى، لعلكم تعقلون؛ فتنزجرون عن ما يضركم.

    Tafsirin As-Sa'di, Larabci v1.0.0, QuranEnc.com

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 72 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri

Tafsiri

Sura ta gabaAal Imranآل عمران

Ba da rahoton kuskure

Ƙari