Hadisai

Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani daga yin tsarki da toroson dabbobi ko ƙashi

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neDar Al-Kutni ne Ya Rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: إِنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ نَهَى أَنْ يُسْتَنْجَى بِرَوْثٍ أَوْ عَظْمٍ، وَقَالَ: «إِنَّهُمَا لَا تُطَهِّرَانِ».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani daga yin tsarki da toroson dabbobi ko ƙashi, kuma ya ce: «‌Lallai su basa tsarkakewa».

Sharhi

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana wanda ya biya buƙatarsa na fitsari ne ko bahaya ya yi tsarkin hoge da ƙashin dabbobi ko torosonsa da busassun torosonsa; kuma ya ce: Lallai su basa kawar da najasa, kuma ba'a tsarkaka daga garesu.

Fa'idoji

  • Bayanin wasu daga cikin ladubban bayan gida da kuma tsarki.
  • Hani daga tsarkin hoge da toroson dabbobi; domin cewa shi: Kodai ya zama najasa, ko kuma domin cewa shi abincin dabbobin aljanu ne.
  • Hani akan yin tsarkin hoge da ƙashi; domin cewa shi kodai najasa ne, ko kuma domin abincin aljanu ne su da kansu.
Sharhi: العربية

نهى النبي صلى الله عليه وسلم مَن قضى حاجته من بول أو غائط أن يستَجْمِر بعظم الحيوان أو روثه وفضلاته الجافّة؛ وقال: إنها لا تزيل النجاسة، ولا تطهر منها.

  • بيان بعض آداب الخلاء والاستنجاء.
  • النهي عن الاستجمار بالروث؛ لأنه: إما نجس، وإما لأنه عَلَفُ دوابِّ الجن.
  • النهي عن الاستجمار بالعظم؛ لأنه إما نجس، وإما لأنه طعام الجن أنفسهم.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari