Hadisai

Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya fito daga bayan gida yana cewa: "Ina neman gafararKa

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neAbu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المؤْمنينَ رَضيَ اللهُ عنها: أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ إِذَا خَرَجَ مِنَ الغَائِطِ قَالَ: «غُفْرَانَكَ».

Fassara

Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita -: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya fito daga bayan gida yana cewa: "Ina neman gafararKa".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya fito daga biyan buƙatarsa na bayan gida yana cewa: Ina roƙonKa (gafararKa) ya Allah.

Fa'idoji

  • An so faɗin: "Ina neman gafafarKa" bayan fitowa daga wurin biyan buƙata.
  • Neman gafarar da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi ga Ubangijinsa a dukkanin halaye.
  • An ce: A cikin sababin neman gafara bayan biyan buƙata: Don taƙaitawa ne a cikin godiyar ni'imomin Allah masu yawa , daga cikinsu akwai sawwaƙa fitar abinda yake cutarwa, kuma ina neman gafararKa dan na shagalta daga anbatanKa a lokacin biyan buƙata.
Sharhi: العربية

كانَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم إذا خَرَجَ مِن قَضاء حاجتِه مِن الغائط قال: أسألُك (غُفرانَك) يا الله.

  • استحباب قول: "غُفرانَك" بعد الخروج من مَحلِّ قضاء الحاجة.
  • استغفار النبيِّ صلى الله عليه وسلم لربّه في جميع الأحوال.
  • قيل في سبب طلب المغفرة بعد قضاء الحاجة: من التقصير في شكر نعم الله الكثيرة ومنها تيسير خروج ما يؤذي، وأطلب مغفرتَك أن انشغلت عن ذكرِك وقت قضاء الحاجة.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari