Hadisai

Gangaran a karatun Alƙur'ani yana tare da manyan mala'iku masu biyayya ga Allah, kuma wanda yake karanta Alƙur'ani kuma yake guragura a cikinsa yana mai shan wuya to yana da lada biyu

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ عَائِشَةَ رضي الله عنها قَالَتْ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «الْمَاهِرُ بِالْقُرْآنِ مَعَ السَّفَرَةِ الْكِرَامِ الْبَرَرَةِ، وَالَّذِي يَقْرَأُ الْقُرْآنَ وَيَتَتَعْتَعُ فِيهِ، وَهُوَ عَلَيْهِ شَاقٌّ، لَهُ أَجْرَانِ».

Fassara

Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Gangaran a karatun Alƙur'ani yana tare da manyan mala'iku masu biyayya ga Allah, kuma wanda yake karanta Alƙur'ani kuma yake guragura a cikinsa yana mai shan wuya to yana da lada biyu.

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda yake karanta Alƙur'ani, alhali shi mai kyakkyawar hadda ne mai kyautatawa, kuma gwani haziƙi a karanta shi, to a lahira yana da ladan da zai zama a matsayinsa tare da manyan mala'iku matafiya masu karamci. Kuma wanda yake karanta Alƙur'ani yake guragura a cikinsa yana kaikawo a karanta shi; dan raunin haddarsa alhali shi tare da hakan yana riƙe da shi, kuma yana wahalar da shi to shi yana da lada biyu; ladan karatun Alkur'ani da kuma ladan wahala da kaikawo a cikin karanta shi.

Fa'idoji

  • Kwaɗaitarwa akan haddace Alƙur'ani da kyautata shi da yawaita karanta shi dan samun lada da sakamako, da kuma bayanin ɗaukakar matsayin wanda ya aikata hakan.
  • Alƙali ya ce: Ba wai ma'anarsa cewa wanda yake guragura gurin karanta shi ya fi gwani lada ba, kai gwani ya fi yawan lada; domin shi gwani yana tare da mala'iku matafiya kuma yana da ladaddaki mai yawa, kuma bai ambaci wannan matsayin ga waninsa ba, to kuwa ta yaya wanda bai kula da Littafin Allah - Maɗaukakin sarki - ba da haddace shi da kyautata shi da yawan karanta shi da dirayarsa hakikanin kulawarsa har ya zama gwani a cikinsa zai riske shi.
  • Ibnu Baaz ya ce: Wanda yake karanta Alƙur'ani alhali shi gwani ne a cikinsa, yana kyautata karatunsa, kuma yana haddarsa da kyau yana tare da mala'iku matafiya masu daraja, yana nufin: Idan ya kasance yana karanta shi a faɗa da aiki, ba wai mujarradin karantawar kawai ba, yana kyautata karatunsa kuma yana aiki da shi, shi yana tsaye da shi a lafazi da ma'ana.
Sharhi: العربية

أخبر النبي صلى الله عليه وسلم أن الذي يقرأ القرآن، وهو جيّد الحفظ مُتقن له، وماهر وحاذق بقراءته، له من الثواب في الآخرة أن تكون منزلته مع الملائكة السفرة الكرام البررة، وأن الذي يقرأ القرآن ويتتعتع فيه ويتردد في تلاوته؛ لِضَعف حفظه وهو مع ذلك يتعاهده، وهو عليه شديد وشاقٌّ فله أجران؛ أجر بالقراءة وأجر للمشقة وتردده في تلاوته.

  • الحث على حفظ القرآن وإتقانه وكثرة تلاوته لنوال الأجر والثواب، وبيان علو منزلة من فعل ذلك.
  • قال القاضي: وليس معناه أن الذي يتتعتع عليه له من الأجر أكثر من الماهر به، بل الماهر أفضل وأكثر أجرًا؛ لأنه مع السفرة وله أجور كثيرة، ولم يذكر هذه المنزلة لغيره، وكيف يلحق به من لم يعتنِ بكتاب الله تعالى وحفظه وإتقانه وكثرة تلاوته ودرايته كاعتنائه حتى مَهَرَ فيه.
  • قال ابن باز: الذي يقرأ القرآن وهو ماهِرٌ فيه، يُجيد قراءَته، ويحفظه جيدًا مع السَّفَرة الكرام البَرَرة، يعني: إذا كان يتلوه قولًا وعملًا، لا مجرّد التلاوة فقط، يُجيد تلاوته، ويعمل به، فهو قائم به لفظًا ومعنًى.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari