Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنْ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «قَالَ اللَّهُ تَبَارَكَ وَتَعَالَى: أَعْدَدْتُ لِعِبَادِي الصَّالِحِينَ، مَا لاَ عَيْنٌ رَأَتْ، وَلاَ أُذُنٌ سَمِعَتْ، وَلاَ خَطَرَ عَلَى قَلْبِ بَشَرٍ» قَالَ أَبُو هُرَيْرَةَ: اقْرَؤُوا إِنْ شِئْتُمْ: {فَلاَ تَعْلَمُ نَفْسٌ مَا أُخْفِيَ لَهُمْ مِنْ قُرَّةِ أَعْيُنٍ} [السجدة: 17].
Fassara
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - Ya ce: Na tanadarwa bayiNa na gari, abinda wani ido bai taɓa gani ba, kunne bai taɓa ji ba, kuma bai taɓa ɗarsuwa a zuciyar wani ɗan Adam ba» Abu Huraira ya ce: Idan kun so ku karanta: {Wata rai ba ta sanin abinda aka ɓoye musu na abinda rai yake farin ciki da shi} [al-Sajdah: 17].
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - Ya ce: Na tanadarwa bayiNa na gari dan girmamawa a cikin aljanna abinda wani ido bai taɓa ganin zatinsa ba, kuma wani kunne bai taɓa jin siffarsa ba, kuma haƙiƙaninsa bai taɓa afkuwa ko wucewa akan zuciyar wani ɗan Adam ba. Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Idan kun so ku karanta: {Wata rai ba ta sanin abinda aka ɓoye musu na abinda rai yake farin ciki (da shi)} [al-Sajda: 17].
Fa'idoji
- Wannan Hadisin yana daga abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yake ruwaito shi daga Ubangijinsa, ana ambatonsa da Hadisi Ƙudsi, ko Ilahi, shi ne wanda lafazinsa da ma'anarsa daga Allah ne, sai dai shi babu keɓance-keɓancen Alƙur’ani a cikinsa waɗanda ya keɓanta da su daga waninsa, kamar bauta da karanta shi, da yin alwala sabo da taɓa shi da fito na fito(ƙalubalanta) da gajiyarwa, (Mu’ujiza) da sauransu.
- Kwaɗaitarwa akan ayyukan ɗa'a da barin ayyukan ƙi; dan rabauta da abinda Allah Ya tanadar da shi ga bayinSa na gari.
- Allah - Maɗaukakin sarki - bai tsinkayar da mu ba a cikin LittafinSa da sunnar ManzonSa akan dukkan abinda ke cikin aljanna, kuma abinda bamu san shi ba, ba shi ne mafi girma daga abinda muka san shi ba.
- Bayanin cikar ni'imar aljanna, kuma cewa ma'abotanta suna samun farin cikin da ya wofinta daga gurɓata ko rashin jin daɗi.
- Jin daɗin rayuwar duniya mai gushewa ne lahira kuwa ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa.
Sharhi: العربية
أخبر النبي صلى الله عليه وسلم أن الله تبارك وتعالى قال: هيّأت وأعددت تشريفًا لعبادي الصالحين في الجنة ما لم يبصر ذاته عين، ولا سمعت وصفه أذنٌ، ولا وقع ولا مر على قلب بشر ماهيته. قال أبو هريرة رضي الله عنه: اقرؤوا إن شئتم: {فَلَا تَعْلَمُ نَفْسٌ مَا أُخْفِيَ لَهُمْ مِنْ قُرَّةِ أَعْيُنٍ} [السجدة: 17].
- هذا الحديث مما يرويه النبي صلى الله عليه وسلم عن ربه، ويسمى بالحديث القدسي أو الإلهي، وهو الذي لفظه ومعناه من الله، غير أنه ليست فيه خصائص القرآن التي امتاز بها عما سواه، من التعبد بتلاوته والطهارة له والتحدي والإعجاز وغير ذلك.
- الحث على عمل الطاعات وترك المنكرات؛ للفوز بما أعده الله لعباده الصالحين.
- الله تعالى لم يُطلعنا في كتابه وسُنَّة رسوله على كل ما في الجَنَّة، وأنَّ ما لم نعلمه أعظم مما عَلِمْنَاه.
- بيان كمال نعيم الجَنَّة، وأن أهلها يَجدون من المَسَرَّات الخَالية من كَدر أو قَلق.
- مَتَاع الدنيا زائل والآخرة خيرٌ وأبقى.