Hadisai

‌Alƙiyama ba zata tashi ba har sai mutane sun dinga yin alfari da massalatai

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neAbu Dawud da Nasa'i da ibn Majah ne Suka Rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَنَسٍ رَضيَ اللهُ عنه أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «لَا تَقُومُ السَّاعَةُ حَتَّى يَتَبَاهَى النَّاسُ فِي الْمَسَاجِدِ».

Fassara

Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «‌Alƙiyama ba zata tashi ba har sai mutane sun dinga yin alfari da massalatai».

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa: Yana daga cikin alamomin kusancin ranar alƙiyama da kuma ƙarewar duniya mutane zasu dinga alfahari da ƙawata masallatansu, ko kuma alfaharinsu da duniyarsu a cikin masallatan da ba'a ginasu ba sai dan ambatan Allah.

Fa'idoji

  • Haramcin yin alfahari da masallatai, kuma hakan aiki ne ba karɓaɓɓe ba; domin ba'a aikata shi saboda Allah ba.
  • Hani daga ƙawata masallatai da kaloli, da kuma fenti kala-kala da kuma zane-zane, da rubce-rubuce; dan abinda ke cikinsu na shagaltar da masallata a yayin kallonsu.
  • Sindi ya ce: Wannan hadisin yana daga abinda duniya ta yi masa shaida, kuma hakan yana daga cikin jumlar mu'ujizoji bayyanannu gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Sharhi: العربية

يخبر النبي صلى الله عليه وسلم: أن من علامات قرب يوم القيامة وانتهاء الدنيا تفاخر الناس بزخرفة مساجدهم، أو تفاخرهم بدنياهم داخل المساجد التي لم تبنَ إلا لذكر الله.

  • تحريم التَّباهي بالمساجد، وأنه عَمل غير مقبول؛ لأنَّه لم يُعمل لله.
  • النَّهي عن زَخْرَفة المساجد بالألوان والأصْبَاغ والنُّقوش، والكتابات؛ لما فيها من إشغال المصلين عند النظر إليها.
  • قال السندي: ‏هذا الحديث مما يشهد بصدقه الوجود، فهو من جملة المعجزات الباهرة له صلى الله عليه وسلم.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari