Hadisai

An umarceni in yi sujjada akan gabbai bakwai

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عن ابنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما عن النبيِّ صلى الله عليه وسلم قال: «أُمِرْتُ أَنْ أَسْجُدَ عَلَى سَبْعَةِ أَعْظُمٍ: عَلَى الْجَبْهَةِ وَأَشَارَ بِيَدِهِ عَلَى أَنْفِهِ، وَالْيَدَيْنِ، وَالرُّكْبَتَيْنِ، وَأَطْرَافِ الْقَدَمَيْنِ، وَلَا نَكْفِتَ الثِّيَابَ وَالشَّعَرَ».

Fassara

Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "An umarceni in yi sujjada akan gabbai bakwai: Akan goshi sai ya yi nuni da hannunsa akan hancinsa, da hannaye, da gwiwoyi, da gefunan diga-digai, kuma kada ka tufke tufafi ko gashi".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa Allah Ya umarce shi a yayin sallah ya yi sujjada akan gabbai bakwai na jiki; su ne: Na farko: Goshi: Shi ne: Fatar fuska a saman hanci da idanuwa, Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi nuni zuwa hancinsa, yana mai bayyana cewa goshi da hanci gaba daya ce daga bakwan, da kuma karfafa cewa mai sujjada yana shafar kasa da hancinsa. Gaba ta biyu da ta uku: Hannaye. Ta hudu da ta biyar: Gwiwoyi. ta shida da ta bakwai: 'Yan yatsun diga-digai. Kuma ya umarcemu kada mu daure gashin mu, ko mu tattaro tufafinmu sashinsu akan sashi a yayin sujjada akan kasa dan karesu; kai ya sake su har su sauka a kasa, sai ka yi sujjada tare da gabbai.

Fa'idoji

  • Wajabcin yin sujjada a cikin sallah akan gabbai bakwai.
  • Karhancin tattaro tufafi da gashi a cikin sallah.
  • Yana wajaba akan mai sallah ya natsu a cikin sallarsa, hakan ya sanya gabban sujjada guda bakwai akan kasa, ya tabbata akansu har ya zo da zikirin da aka shara'anta.
  • Hani daga kame gashi (wannan) ya kebanci maza banda mata; domin cewa mace a cikin sallah abar umarta ce da sutaurtawa.
Sharhi: العربية

بَيَّنَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم بأنَّ اللهَ أَمَرَه عند الصلاة أنْ يَسجُدَ على سبعةٍ من أعضاء الجسم؛ وهي: أولاً: الجبهة: وهي: صفحة الوجه فوق الأنف والعينين، وأشار صلى الله عليه وسلم بيده إلى أنفِه، مُبَيِّنًا أن الجَبْهةَ والأنف عضو واحد من السبعة، وتأكيدًا على أنَّ الساجِد يُلامِسُ بأنفِه الأرضَ. العضو الثاني والثالث: اليدان. الرابع والخامس: الرُّكْبتان. السادس والسابع: أصابع القدمين. وأَمَرَنا أنْ لا نَربِطَ شعورنًا، أو نَجمعَ ثيابَنا بعضَها على بعض عند السجود على الأرض صيانةً لها؛ بل نُرسِلُها حتى تقع على الأرض، فتسجد مع الأعضاء.

  • وجوب السُّجود في الصلاة على الأعَضاء السَّبعة.
  • كراهية جَمْعِ وضَمِّ الثَّوب والشَّعَر في الصلاة.
  • يجب على المصلي أن يطمئن في صلاته، وذلك بأنْ يضع أعضاء السجود السبعة على الأرض، ويستقر عليها حتى يأتي بالذكر المشروع.
  • النهيُ عن كَفِّ الشَّعَرِ خاصٌّ بالرجال دون النساء؛ لأن المرأة في الصلاة مأمورة بالتستر.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari