Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنِ الْبَرَاءِ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِذَا سَجَدْتَ، فَضَعْ كَفَّيْكَ وَارْفَعْ مِرْفَقَيْكَ».
Fassara
Daga Bara'u - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce -: "Idan zaka yi sujjada, to ka sanya tafukanka ka kuma ɗaga gwiwowin hannunka".
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana halin hannaye a cikin sujjadar sallah, hakan da ya tabbatar da tafukansa a ƙasa kuma ya ɗora yatsun a ɗunƙule a fuskantar alƙibla, kuma gwiwowin hannaye - sune mararrabar zira'i da damutse - a ɗage daga taɓ ƙasa kuma a buɗe daga sasanni.
Fa'idoji
- Wajibi akan mai sallah ya ɗora tafukansa akan ƙasa, tafuka biyu gaɓɓai ne daga gaɓɓan sujjada guda bakwai.
- An so ɗaga zira'i biyu daga ƙasa, da karhancin shinfiɗasu kamar yadda zaki yake shinfiɗa zira'ansa biyu.
- Halaccin bayyanar da nishaɗi da ƙarfi da kwaɗayi a cikin ibada.
- Mai yin sallah idan ya dogara akan dukkan gaɓɓan sujjada, to kowace gaɓa zata riƙi haƙƙinta na ibada.
Sharhi: العربية
بَيَّنَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم حالةَ اليدين في سجود الصلاة، وذلك بأن يُمَكِّنَ الكفَّين من الأرض ويضعها مضمومة الأصابع في اتجاه القبلة، ويكون المرفقان -مفصل الذراع والعضد- مُرتَفعَين عن ملامسة الأرض ومُفرجين عن الجنبين.
- الواجب على المصلِّي أن يَضع كفَّيه على الأرض، والكفان عُضوان من أعضاء السُّجود السَّبعة.
- استحباب رفع الذِّراعين عن الأرض، وكراهة افتراشهما كما يَفترش السَّبع ذِراعيه.
- مشروعية إظهار النَّشاط والقوَّة والرَّغبة في العَبادة.
- المُصلِّي إذا اعتمد على جميع أعضاء السُّجود، أخذ كلُّ عُضوٍ حقَّه من العبادة.