Hadisai

Na yi sallah tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya kasance yana yin sallama a damansa: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh. "Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa", kuma a hagunsa: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh. "Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Hasan neAbu Dawud ne Ya Rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ وَائِل بن حُجرٍ رضي الله عنه قَالَ: صَلَّيْتُ مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَكَانَ يُسَلِّمُ عَنْ يَمِينِهِ: «السَّلَامُ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَةُ اللَّهِ وَبَرَكَاتُهُ»، وَعَنْ شِمَالِهِ: «السَّلَامُ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَةُ اللَّهِ».

Fassara

Daga Wa'il ɗan Hujur - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na yi sallah tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya kasance yana yin sallama a damansa: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh. "Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa", kuma a hagunsa: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh. "Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah".

Sharhi

Annabin - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya yi nufin ya juya daga sallarsa zai yi sallama a damansa da hagunsa shi ne ya juyar da fuskarsa ɓangaren dama, tare da faɗinsa: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh. (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa), kuma yana yin sallama a hagunsa, shi ne ya juyar da fuskarsa ɓangaren hagu, tare da faɗinsa: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh. (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah).

Fa'idoji

  • Halaccin sallama biyu a sallah, kuma ita tana daga rukunanta.
  • An so zuwa da ƙarin faɗin: (Da albarkarSa), a sashin lokuta; domin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance yana dawwama akanta ba.
  • Furta sallama biyu a cikin sallah rukuni ne na wajibi, amma yin waiwaye a tsakiyar furta su to (Mustahabbi ne) abin so ne.
  • Yana kamata ya ce: (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah) a tsakiyar yin waiwaye ba kafinsa ko bayansa ba.
Sharhi: العربية

كَانَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم إذا أراد أنْ يَنصَرِفَ من صلاته سلَّم عن يمينه وشماله بأن يلتفت بوجهه للجهة اليمنى، مع قوله: (السلام عليكم ورحمة الله وبركاته)، ويسلِّم عن شماله، بأن يلتفت بوجهه للجهة اليسرى، مع قوله: (السلام عليكم ورحمة الله).

  • مشروعية التسليمتين من الصلاة، وأنها من أركانها.
  • استحباب الإتيان بزيادة قول: (وبركاته)، في بعض الأحيان؛ لأن النبي صلى الله عليه وسلم لم يكن يُدَاوِم عليها.
  • النطق بالتسليمتين في الصلاة ركن واجب، وأما فعل الالتفات أثناء النطق بهما مستحب.
  • ينبغي أن يكون قول: (السلام عليكم ورحمة الله) أثناء فعل الالتفات لا قبله ولا بعده.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari