Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عن جابر رضي الله عنهما قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «لن يدخلَ النارَ رجلٌ شَهِد بدرًا والحُدَيْبِيَة».
Fassara
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Duk mutumin da ya halarci (yaƙin) Badar da Hudaibiyya ba zai shiga wuta ba".
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa duk wanda ya halarci yaƙin Badar wanda aka yi a cikin shekara ta biyu da hijira yana mai yaƙi tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, haka nan wanda ya halarci Sulhun Hudaibiyya, kuma a cikinsa ne aka yi Bai'atir Ridwan wacce aka yi a cikin shekara ta shida da hijira ba zai shiga wuta ba.
Fa'idoji
- A cikinsa akwai falalar ma'abota (yaƙin) Badar da Hudaibiyya, kuma su ba zasu shiga wuta ba.
- Bayanin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Zai lamunce musu abinda ake bin su, kuma Zai datar da su ga mutuwa akan imani, kuma Zai shigar da su aljanna ba tare da rigayar azabar wuta ba, wannan kuma falalar Allah ce da yake ba wa wanda Yake so, Allah Ma'abocin falala ne Mai girma.
Sharhi: العربية
أخبر النبي صلى الله عليه وسلم أنه لن يدخل النار من حَضَرَ غزوة بدر التي وقعت في السنة الثانية من الهجرة مقاتلًا مع النبي صلى الله عليه وسلم، ولا من حضر صلح الحديبية، وفيه بيعة الرضوان التي وقعت في السنة السادسة من الهجرة.
- فيه فضيلة أهل بدر والحديبية، وأنهم لن يدخلوا النار.
- بيان أن الله تعالى يضمن عنهم المظالم، ويوفقهم للموت على الإيمان، ويدخلهم الجنة بلا سَبْقِ عذاب النار، ذلك فضل الله يؤتيه من يشاء، والله ذو الفضل العظيم.