Hadisai

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya cewa Abubakar da Umar: "Waɗannan biyun sune shugabannin dattijan 'yan aljanna daga na farko dana ƙarshe sai dai Annabwa da Manzanni

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neTirmizi ne ya ruwaito shi

Rubutun Larabci

عن أنس رضي الله عنه، قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم لأبي بكر وعمر: «هذان سَيِّدا كُهُول أهل الجنة من الأوَّلِين والآخِرين إلا النبيِّين والمرسلين».

Fassara

Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya cewa Abubakar da Umar: "Waɗannan biyun sune shugabannin dattijan 'yan aljanna daga na farko dana ƙarshe sai dai Annabwa da Manzanni".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Abubakar Siddiƙ da Umar Faruƙ - Allah Ya yarda da su - sune mafifitan mutane bayan Annabawa, kuma mafifitan waɗanda suka shiga aljanna bayan Annabwa da Manzanni.

Fa'idoji

  • Abubakar da Umar - Allah Ya yarda da su - sune mafifitan mutane bayan Annabawa da Manzanni.
  • A aljanna babu tsoho, kai, wanda zai shigeta ɗan shekara talatin da uku ne, abin nufi cewa sune shugabannin wanda ya mutu yana dattijo a duniya, ko kuma hakan izina ne na abinda suke akansa a duniya a lokacin wannan hadisin.
Sharhi: العربية

أَخْبَرَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ أبا بكر الصديق وعمر الفاروق رضي الله عنهما هما أفضل البشر بعد الأنبياء، وأفضل مَن دخل الجنة بعد النبيين والمرسلين.

  • أبو بكر وعمر رضي الله عنهما هما أفضل الناس بعد الأنبياء والمرسلين.
  • ليس في الجنة كَهْلٌ، بل مَن يدخلها ابن ثلاث وثلاثين سنة، والمراد أنهما سيدا مَن مات كهلًا في الدنيا، أو أنّ ذلك باعتبار ما كانوا عليه في الدنيا حال هذا الحديث.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari