Hadisai

Alhasan da Alhusain su ne shugabannin matasan 'yan Aljanna

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neTirmizi da Ahmad sun rawaito shi

Rubutun Larabci

عن أبي سعيد الخدري رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «الحَسَن والحُسَيْن سَيِّدا شَباب أهْل الجنة».

Fassara

Daga Abu Sa'idu Khudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Alhasan da Alhusain su ne shugabannin matasan 'yan Aljanna".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa jikokinsa biyu Alhassan da Alhussain 'ya'yan Ali ɗan Abu Ɗalib da Faɗima 'yar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma Allah Ya yarda da su -, su ne shugabannin wanda ya mutu a falala alhali shi yana saurayi kuma ya shiga aljanna, ko cewa sune shugabannin matasan 'yan aljanna in an cere Annabawa da Khalifofi Masu shiryarwa.

Fa'idoji

  • A cikinsa akwai falala ta zahiri ga Hassan da Hussain - Allah Ya yarda da su -.
  • An ce a cikin ma'anar hadisin: Cewa su a lokacin hadisin sune shugabannin waɗanda sune daga 'yan aljanna cikin matasan wannan zamanin, ko kuma cewa sune mafifita daga waɗanda falala mai gamewa ba ta tabbata a cikinsa ba kamar Annabawa da Khalifofi, ko kuma cewa sune shugabannin waɗanda suka siffantu da siffofin samartaka da yarinta kamar karamci da gwarzantaka, kuma bai zo da shekarun matasa da hakan ba; domin Hassan da Hussain sun mutu alhali suna gwaraza.
Sharhi: العربية

أَخْبَرَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ حَفيدَيه الحسن والحسين ابنا علي بن أبي طالب وفاطمة بنت النبي صلى الله عليه وسلم ورضي عنهم، هما سيدا كلِّ مَن مات وهو شاب ودخل الجنة في الفضل، أو أنهما سيدا شباب أهل الجنة باستثناء الأنبياء والخلفاء الراشدين.

  • فيه فضيلة ظاهرة للحسن والحسين رضي الله عنهما.
  • قيل في معنى الحديث: أنهما في وقت الحديث هما سيدا شباب مَن هم من أهل الجنة من شُبّان هذا الزمان، أو أنهما أفضل ممن لم يثبت فيه تفضيلٌ عامٌّ كالأنبياء والخلفاء، أو أنهما سيدا من اتصف بصفات الشباب والفُتُوَّة كالمروءة والكرم والشجاعة، ولم يَرِدْ بذلك سِنَّ الشباب؛ لأن الحسن والحسين ماتا كَهْلَين.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari